Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-24 14:18:14    
Kasar Afirka ta kudu ta samu ci gaba da sauri wajen bunkasa masana'antun kasa da kasa

cri
Daga cikin kamfanonin kasa da kasa 50 da aka ambata sunayensu cikin rahoton babban taron ciniki da bunkasuwa na MDD, wadanda kuma suke jawo hankulan kasashen duniya, har da guda 7 na kasar Afirka ta kudu ne. Ko a kasashe masu ci gaba ma wadannan kamfanoni suna da babban karfin yin gasa a tsakaninsu.

Daga cikin wadannan kamfanoni, kamfanin Angolo American PLC da na De Beers da ke Afirka ta kudu sun riga sun zama hamshakan kamfanonin hakan ma'adainai. Kamfanin yin giya na Afirka ta kudu ya shiga cikin jerin masana'antun yin giya mafi girma na duniya. Kamfanin Sappi kuma yana daya daga cikin masana'antun yin takardu mafi girma na duk duniya. Kamfanin MTN ba ma kawai yana gudanar da harkokinsa a duk Afirka ba, har ma yana mallakar wasu kasuwannin Turai da nahiyar Amirka da na Asiya, Kamfanin MDDAS ta riga ta sayar da kayyyakinsa cikin kasuwannin kasashe da shiyyoyi fiye da 40 na duniya.

Dalilin da ya sa kasar Afirka ta kudu ta samu nasara wajen bunkasa masana'antun kasa da kasa shi ne sabo da ya kasance da tsari mai ci gaga wajen gudanar da harkoki, da yin ciniki da musanyar kudi cikin 'yanci a kasar, kuma ana yin hadima mai kyau wajen sha'anin kudi, da kuma gudanar da harkokin kudi daidai kamar yadda ake yi a kasashen duniya. Domin kara karfin shiga cikin kasuwannin kasashen duniya, da farko masana'antun Afirka ta kudu sukan sayi wasu kamfanoni a cikin kasar, bayan da suka shiga cikin kasuwannin kasashen duniya kuma, kamfanonin kasa da kasa da yawa da ke Afirka ta kudu sukan sayar da wasu kamfanoni marasa muhimmanci, kuma a kai a kai ne suka zama kamfanonin da suke mallakar wasu kasuwannin musamman na duk duniya.

Domin daidaita wasu matsalolin da wadannan kamfanonin kasa da kasa da ke Afirka ta kudu ke gamuwa da su cikin kasuwannin kasashen duniya, sukan sayi masana'antu da yawa daga kasashen ketare. Alal misali, kamfanin yin giya na Afirka ta kudu ya sayi kamfanin yin giya mallakar gwamnatin Tanzaniya, kamfanin De Beers ya sayi kuma ya yi garambawul ga kamfanin lu'u-lu'u na kasar Namibia.

Hukumomin kudi na Afirka ta kudu su ma sun nuna babban goyon baya ga masana'antun kasa da kasa da ke kasar wajen kudi. "Bankin raya Afirka da ke Afirka ta kudu" ya nuna babban goyon bayansa ga masana'antun kasa da kasa da ke Afirka ta kudu da su gudanar da harkokinsu a kasashen duniya, musamman ma a shiyyoyin da ke kudancin Afirka har da dukkan yankunan Afirka baki daya daga fannin yin hidima wajen makamashi da sadarwa, da samar da ruwa, da sufuri da yawon shakatawa da kuma kudi. Kamfanonin kasa da kasa da ke Afirka ta kudu wajen kudi da makamashi da sadarwa da hakar ma'adinai dukkansu sun samu nasara wajen mallakar kasuwannin Afirka da farko, daga baya kuma sun juya hankulansu don mallakar sauran kasuwannin kasashen duniya. Wadannan kamfanonin kasa da kasa ba ma kawai sun zama masu zuba jari mafi girma ga babban yankin Afirka ba, hatta ma kashi 85 cikin 100 bisa dukkan masu zuba jari na kasashen waje sun riga sun juya hankulansu kan kasuwannin Turai da na nahiyar Amurka.

Cikin shekaru kusan 10 da suka wuce, tattalin arzikin Afirka yana ta samun bunkasuwa mai dorewa, wannan ya kawo sharuda masu amfani ga Afirka ta kudu wajen bunkasa masana'antunta na kasa da kasa. Sassan ba da shawara kan harkokin tattalin arzikin Afirka su ma sun sa ran alheri ga makomar samun bunkasuwa ta masana'antu kasa da kasa da ke Afirka ta kudu. (Umaru)