Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-24 13:25:53    
Hu Jintao yana fatan 'yan wasan kasar Sin za su sami sakamako mai kyau a duk fannin gasa da ruhu na wayewar kai

cri

Ran 23 ga wata a birnin Beijing, Mr. Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasa ya bayyana cewa, yana fatan 'yan wasan kasar Sin za su sami sakamako mai kyau a duk fannin gasa da na ruhun wayewar kai.

Ran 23 ga wata, Mr. Hu da sauran shugabanni sun zo hukumar horo ta hukumar harkokin wasannin motsa jiki ta kasar Sin domin sa ido kan ayyukan shirya gasar wasannin Olympic, da kuma kai wa 'yan wasa da masu horo da ma'aikata ziyara, kuma ya yi fatan alheri ga dukansu a madadin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.

A karshe kuma Mr, Hu ya furta cewa, yana fatan hukumar harkokin wasannin motsa jiki ta kasar Sin za ta dauki muhimmanci kan hora kafin gasar, ta yadda 'yan wasa za su halarci gasa cikin hali mafi kyau, kuma a mai da hankali kan aikin tunani, ta yadda 'yan wasa za su iya nuna kyakkyawan halin zuciya wajen halartar gasa. Kuma a mai da hankali kan aikin ba da guzuri, ta yadda 'yan wasa za su samu hali mai kyau a lokacin shirya da kuma halartar gasa.(Fatima)