Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-23 21:05:52    
Ana nuna rashin kula da cututtukan tunani har kullum

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na "ilmin zaman rayuwa". Ni ce Kande ke gabatar muku da wannan shiri. A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku wani bayani kan cewa, ana nuna rashin kula da cututtukan tunani har kullum.

Kwararrun kasar Amurka wajen cututtukan tunani sun gudanar da wani bincike ga fararen hula wajen lafiyar tunaninsu, kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, 'yan Amurka da yawansu ya kai kusan kashi 30 cikin dari suna fama da cututtukan tunani iri daban daban, amma sulusi daga cikinsu ne kawai suka je asibiti wajen ganin likita. Sabo da haka kwararru sun yi kira ga dan Adam da su kula da lafiyar tunani, muddin sun kamu da cututtukan tunani, ya kamata su yi iyakacin kokarinsu wajen ganin likita.

Kungiyar bincike da ke karkashin jagorancin likita Eric Messias na kwalejin ilmin likitancin na jihar Georgia na kasar Amurka ta ba da rahoton, cewa sun gudanar da wani bincike ga mutane 816 na birnin Baltimore na jihar Maryland na Amurka daga shekara ta 1993 zuwa shekara ta 1999. Kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, a cikin cututtukan tunani iri daban daban da suke bukatar warkarwa, mutanen da suke fama da cutar dogaro da shan giya su ne mafi yawa, wato ya kai kashi 14 cikin dari, na biyu shi ne mutanen da suke fama da cutar bakin ciki, wato ya kai wajen kashi 11 cikin dari. Ban da wannan kuma mutane masu yawa suna kamuwa da cutar jin tsoro da cutar tsoron yin mu'amala da sauran mutane.

Likita Messias ya yi hasashen cewa, bisa wanann binciken da aka gudanar, an gano cewa, mutane da yawa suna bukatar a yi musu jiyya wajen lafiyar tunani, amma kullum ana nuna rashin kula da wadannan cututtuka. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da wasu mutane suna ganin cewa, ana iya warkar da cututtukan tunani da kansu, kuma ba a bukatar ganin likita. Wasu mutane kuwa suna ganin cewa, ba a iya warkar da cututtukan tunani kwata kwata ba, ban da wannan kuma wasu mutanen da suke fama da cututtukan ba su son ganin likita domin matsin lamba da suka samu daga zaman al'umma ko kuma domin kiyaye martabobinsu. Bugu da kari kuma wasu cututtukan tunani ba su cikin inshorar jiyya, da kuma karancin likitoci masu kula da lafiyar tunani su ma muhimman dalilai ne. manazarta suna ganin cewa, ba tilas ba ne a bukaci shan magunguna wajen warkar da cututtukan tunani, za a iya saussauta cututtukan ta hanyar yin amfani da hankalin mutane.

To, masu sauraro, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu ci gaba da gabatar muku kan yin jiyya kan cutar tunani. Hanyar gargajiya ta yin jiyya kan cutar tunani ita ce kara kwarin gwiwar masu kamuwa da cutar wajen fadin albarkacin bakinsu, amma sabon rahoton binciken da manazarta na kasar Amurka suka gudanar ya nuna cewa, bayan aukuwar mummunan bala'i, mutanen da suka ganam ma idonsu ba safai su kan amince da tattaunawa kan abubuwan da suka ji a rai da kuma ra'ayoyinsu ba, watakila wannan zai ba da taimako wajen kwantar da hankulansu.

Manazarta na reshen jami'ar New York da ke birnin Buffalo na kasar Amurka sun ba da rahoto cewa, bayan da aka kai farmakin ta'addanci ga Amurka a ran 11 ga watan Sabtamba har shekaru biyu, sun gudanar da bincike ga wasu mutanen da suka ganam ma idanunsu kan farmakin ta hanyar Internet domin fahimtar illar da wannan farmakin ta'addanci ya yi wa lafiyar jikinsu da kuma tunaninsu.

Kuma manazarta suna ganin cewa, game da wasu mutanen da suka kamu da cutar tunani, watakila daina fadin albarkacin bakinsa wata hanya ce mafi kyau, wani muhimmin abu na yin jiyya kan cutar tunani shi ne tsara shirye-shiryen jiyya daban daban bisa halayen musamman na mutane daban daban. (Kande Gao)