Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-23 21:03:55    
Wata shaharariyyar zabiya ta kasar Sin mai suna Zheng Xulan

cri

A farkon lokacin da kasar Sin take yin gyare-gayre da bude wa kasashen waje kofa a shekaru 80 na karnin da ya shige, Zabiya Zheng Xulan ta girgiza dukkan mutanen kasar Sin ta hanyar wakokin da ta rera, kodayake ta sha wahaloli da yawa a zaman rayuwa, amma tana kasancewa cikinfarin ciki. Ta ce, tana zaman rayuwa domin wakoki, muddin 'yan kallo suna son wakokinta, to za ta ci gaba da rera wakoki har zuwa ranar shiga gidan gaskiya."

A lokacin da ya wuce ba da dadewa, wato a lokacin bikin gargajiyar kasar Sin na yanayin bazara, Zabiya Zheng Xulan ta rera wata wakar da ta sami suna a karo na farko, wato wakar da ke da lakabin "Waiwayi zaman rayuwata na tamkar malalar ruwa".

Wani malamin da ya yi girma tare da saurarar wakar, kuma aminin Zheng Xulan mai suna Zhang Hanzhong ya bayyana cewa, a wancan lokacin, da na ji wakarta, sai na ji cewa, wakar na da dadin ji sosai, kuma wakar ta jawo sha'awar kowanenmu sosai, mutane da yawa sun je yawon shakatawa musamman a tsibirin rana bayan da suka saurari waka mai suna "a kan tsibirin rana".

A shekarar 1977, Malama Zheng Xulan ta shiga kungiyar yin raye-raye da wake wake ta Dongafang , sa'anan kuma ta zama kwararriyar zabiya sosai wajen rera wakoki, kuma ta yi suna sosai a cikin shekaru da yawa.

Bayan da ta yisuna a ko'ina a kasar Sin, sai zabiyar ta dauki muryar wakoki da yawa a fayafaye, ta taba zuwa kasar Philipings da Malasiya don koyon wakokin gargajiya na kasashen.

A shekarar 1989, Zheng Xulan ta tafi kasar Amurka , inda ta mai da hankali soai ga renon danta. A wannan lokaci, ta kamu da ciwo, kuma an yi mata tiyata har sau biyu, a daidai wannan lokaci kuma , wani namijin da za ta aurar da shi, shi ma ya kamu da ciwon sankara, kai, lamarin nan ya zama abin bakin ciki sosai gare ta, amma a sa'I daya kuma , ta ji ta kara tsayayyar niyyarta, ta bayyana cewa, kowa zai fuskanci wahaloli, amma na da banbanci kawai. Ban taba jin cewa, abu mai ban tausayi gare ni ne kawai ba, kuma ya kamata kowa ya nuna mini tausayi. Na ci gaba da zaman rayuwa ba tare da zuba hawaye ko kadan ba.

Bisa halin nan da take ciki, zabiya Zheng Xulan ba ta rasa hakuri ba, tana ci gaba da rera wakoki ga 'yan kallo, ta ce, dukkan ayyukan da na yi ne domin wakoki. Wakar da ta rera mai suna kurciya, ki tashi fil fil fil.

A cikin wakar, an bayyana cewa, iska ta jure niyyarki, ruwan sama ya wanki fikafikanki. Tashi kike, kurciya mai kaunata, kina tsayawa tsayin daka kan niyyarki . Zabiya Zhen Xulan ta sake fitowa a dakalin nuna wasanni a gaban 'yan kallo na kasar Sin, wakar da take rera tamkar yadda ta yi a da, tana ci gaba da cike da dadin ji. A shekarar 1999, wani basinne da ke zama a kasar Singapour ya taimaki Zheng Xulan da ta rera wakoki dangane da wake-waken "Hongloumeng" wanda aka kiransa "A Dream Of Red Mansions" or "The Story of the Stone", bayan da aka saurari wakokin, sai aka nuna mata yabo sosai, har wa yau dai tana rera wakokin a kan dakalin nuna wasanni na gida da na waje.

Ko a kasashen Turai ko a kasashen da ke arewacin nahiyar Amurka, dukkan wuraren da suka samu Sinawa, wakokin Zheng Xulan sun sami karbuwa sosai. Amma Zhen Xulan ba ta tsaya ba, tana ci gaba da tsara wasu sabbin wakoki, kodayake samari mawaki suna ta kara fitowa, amma tsoffin masu sauraronta suna ci gaba da saurarar wakokinta.(Halima)