Yau 23 ga wata, shugaban sashen kula da harkokin tsaro da ke karkashin jagorancin kwamitin wasannin Olympics na Beijing, Mr.Liu Shaowu ya bayyana cewa, yanzu an riga an fara gudanar da aikin tabbatar da tsaro ga wasannin Olympics daga dukan fannoni.
A gun taron manema labarai da aka kira a ran nan a babbar cibiyar watsa labaran wasannin Olympics na Beijing, Mr.Liu Shaowu ya ce, gwamnatin kasar Sin na dora muhimmanci sosai a kan tabbatar da tsaro ga wasannin Olympics, kuma ta kafa tsarin ba da jagoranci mai inganci, ta kuma tsara shirye-shirye sosai, kuma tana hada gwiwa da gamayyar kasa da kasa a wannan fanni. Ya ce, masu kula da harkokin tsaron wasannin Olympics sun hada da 'yan sanda da sojoji da dai sauransu, bayan haka kuma, an dauki dimbin masu aikin sa kai da su shiga aikin tabbatar da tsaro ga wasannin Olympics.(Lubabatu)
|