JINAN, An kawo karshen yawo da wutar wasannin Olympics a lardin Jinan da ke gabashin kasar Sin a ranar Laraba da misalin karfe 10.45.
Yar wasan ninkaya Guo Jinjin da tsohon zakaran wasan springboard na mita 3 na maza Wang Feng su ne suka kunnan wutar a dandalin Qilu . a matsayinsu na wadanda suka rinke wutar na karshe
Gudun mika wutan wasannan Olympics na Beijing a Jinan shi ne zango na karshe na zagayawa da wutan a lardin Shandong.
An soma gudun mika wutan ne a Shandong ranar Litinin aka kuma ratsa da shi zuwa Tsingdao, Linyi, Qufu da Tai'an a kwanaki biyu da suka wuce.
Yawan wadanda suka shiga aikin gudud da wutan sun kai 832 a jihar Shandong, daga nan ne kuma Wutan zai tashi zuwa jihar Henan. (ilelah)
|