Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-22 19:12:40    
Gasar wasannin Olympic ta Beijing tana bayyana yadda kasar Sin ke samun cigaban kimiyya da fasaha na zamani

cri
A gun wani taron manema labaru da aka yi a watan Mayu na shekarar da muke ciki, Mr. Wan Gang, ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin ya yi bayani cike da imani cewa, "Muna da imanin cewa, gasar wasannin Olympic ta shekara ta 2008 ta birnin Beijing za ta zama wata gasar wasannin Olympic wadda ake amfani da ilmin kimiyya da fasaha na zamani mafi yawa."

Idan ka duba dakuna da filayen wasannin motsa jiki da aka gina domin wannan gasar wasannin Olympic ta Beijing, za ka iya gano cewa, minista Wan Gang, wani masani ne da ya kware kan fasahohin zamani bai yi alfahari ba. Mr. Tan Xiaochun wanda ke kula da aikin gina "Shekar Tsuntsu", wato filin wasannin motsa jiki na kasar Sin ya ce, "Tsawon layin walda na tsarin bakin karfe na 'Shekar Tsuntsu' ya kai kilomita 320, 'yan kwadago masu yin aikin walda 1100 sun yi wannan aiki ne fiye da shekara 1. Wannan kuma wani abin al'ajabi ne a kan tarihin gine-gine na kasar Sin."

Mr. Ren Guozhou, wani tsohon shehu malami na kamfanin masana'antun sararin samaniya na kasar Sin ya ce, "Fitila mai dauke da wuta ba ta iya yin aiki kamar yadda ake fata ba a wurin da ya kai fiye da mita 6500 daga leburin teku. Sabo da haka, mun yi nazari kan fasahar kera fitila mai dauke da irin wuta da za ta iya ci gaba da yin aiki a kolin tsaunin Qomolangma, wato za ta iya yin aiki tun daga wurin da ya kai mita 6500 daga leburin teku zuwa kolin tsaunin Qomolangma."

Haka kuma, Mr. Yang Yichun, shugaban hukumar kimiyya da fasaha ta kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya ce, "Fasahar zamani da muka dauka domin tsaron gasar wasannin Olympic ta Beijing ita ce, fasahar daukar hotuna masu inganci sosai."

Gasar wasannin Olympic ta lokacin yanzu tana bukatar goyon baya daga ilmin kimiyya da fasahohin zamani. "Gasar wasannin Olympic da ke cike da kimiyya da fasaha na zamani" na daya daga cikin tunani uku da ake bi lokacin da ake shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing, kuma wannan ne karo na farko da aka tabbatar da cewa za a yi amfani da kimiyya da fasaha na zamani a gun gasar wasannin Olympic a bayyane. Ilmin kimiyya da fasaha na zamani ba ma kawai suna tabbatar da shirya wata gasar wasannin Olympic mai inganci wadda take da halin musamman ba, har ma za su amfana wa kokarin cika alkawarin aiwatar da wata gasar wasannin Olympic wadda take amfanawa rayuwar dan Adam na yau da kullum, kuma ba tare da gurbata muhalli ba.

Ana ganin cewa, dalilin farko da ya sa za a iya cika alkawarin aiwatar da wata gasar wasannin Olympic da ake amfani da kimiyya da fasaha na zamani shi ne, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai, kuma bangarori daban daban na kasar Sin sun yi kokarin cimma wannan buri tare. A waje daya kuma, wani dalili daban shi ne kasar Sin ta samu babban cigaba a fannonin kimiyya da fasaha na zamani a cikin shekaru 30 da suka gabata bayan da ta soma aiwatar da manufofin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje yau da shekaru 30 da suka gabata. Bugu da kari kuma, wani dalili daban shi ne a cikin wadannan shekaru da yawa da suka gabata, tattalin arzikin kasar Sin ya samu cigaba sosai. Mr. Wan Gang, ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin ya bayyana cewa, "Hukumomin kasar Sin sun aiwatar da shirye-shiryen kimiyya da fasaha guda 10 domin tabbatar da ganin an shirya wata gasar wasannin Olympic mai inganci wadda take da halin musamman. Bayan da aka yi amfani da sabbin fasahohin zamani mai tarin yawa a kan ayyukan motsa jiki na gasar wasannin Olympic ta Beijing, wadannan fasahohin zamani za su kawo mana moriya sosai a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma."

Gasar wasannin Olympic ta Beijing da za a fara yi ba da dadewa ba, ba ma kawai wata kasaitacciyar gasar wasannin motsa jiki ta duk duniya ba, har ma wata dama ce da ke nune-nunen cigaban da kasar Sin ta samu a fannonin kimiyya da fasaha na zamani. A gun wannan gasar, duk duniya za su iya raba sakamakon kimiyya da fasaha da kasar Sin ta samu. Jerin sakamakon kimiyya da fasaha na zamani za su zama dukiya mai daraja da Beijing zai samar wa wasannin motsa jiki na Olympic.  (Sanusi Chen)