
Ran 22 ga wata, an cimma nasarar ayyukan mika wutar wasannin Olympics na Beijing a biranen Qufu da Tai'an na lardin Shandong.

Birnin Qufu kirar "birni mai tsarki na gabas" shi ne garin Confucius wani babban mutum mai akida a tarihin kasar Sin, a sa'i daya kuma birnin Qufu ya haifar da al'adun tunanin Confucius. An fara mika wutar wasannin Olympics a birnin Qufu tun daga karfe 8 a wannan rana da safe, bayan mikawar da mutane 100 suka yi a cikin tsawon lokaci da ya kai awa guda da mintoci 40, wutar ta isa zango na karshe inda mutum mutumin Confuciue ke can.
Bayan kammala aikin mika wutar wasannin Olympics a birnin Qufu, a wannan rana da safe da karfe 11 da rabi an fara mika wutar a birnin Taian, kuma a karshe an isar da wutar a karkashin dutsen Taishan wanda ya fi shahara a kasar Sin kuma ya zama kayayyakin tarihin hallitu na duniya.
|