Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-21 21:10:38    
'Yan wasannin kwallon tebur na kasar Nijeriya suna dauke da nauyin bayyana fatan Afirka a gasar wasan Olympics ta Beijing

cri

Saurari

A darikar wasannin kwallon tebur ta duk duniya, 'yan wasa na Asiya da Turai sun fi kwarewa, har ma a gasar wasan kwallon tebur ta Olympics, ya kan kasance da takara da ke tsakanin 'yan wasanni na Asiya da Turai, ba safai 'yan kallo su kan lura da 'yan wasannin kwallon tebur da suka zo daga Afirka ba. A hakika dai, ya kasance da 'yan wasan kwallon tebur da yawa a nahiyar Afirka, ko da yake ba su samu lambobi ba, amma ra'ayin da suke dauka wajen halartar gasar wasannin Olympics ya shaida cewa, 'yan wasan kwallon tebur na kasar Nijeriya suna dauke da nauyin bayyana fatan Afirka a gasar wasannin Olympics ta Beijing.

'Yan wasannin kwallon tebur na kasar Nijeriya wato Mr. Segun Toriola da Madam Bose Kaffo sun riga sun halarci gasar wasannin Olympics har sau hudu, wannan matsayi ya wuce 'yan wasanni da yawa da ke da kwarewa sosai a fannin wasan kwallon tebur. A halin yanzu dai, Mr. Segun Toriola da Madam Bose Kaffo suna shiryawa domin shiga cikin gasar wasannin Olympics ta Beijing wato za su gudanar da tafiya ta karo ta biyar ta gasar wasannin Olympics.

Madam Bose Kaffo ta gaya mana cewa, 'Dalilin da ya sa na halarci gasannin wasannin kwallon tebur da yawa shi ne, domin ina yin kokari da nake iya yi a yayin da nake yin ko wane irin abu. Wasan kwallon tebur ya zama sha'anina a duk rayuwata. Da na kasance dauke da rakit, to, zan yi kokari sosai domin buga kwallon tebur da kyau. Zan kara karfafa kwarewata da na kara buga shi.'

A matsayin kwallon kasa na Sin, tabbas ne gasar wasannin kwallon tebur za ta jawo hankulan 'yan kallo sosai, Mr. Segun Toriola ya yi imani cewa, kasar Sin za ta shirya wata gasar wasan kwallon tebur da ta fi cin nasara a duk tarihin Olympics. Ya ce, 'Ina da imanin cewa, kasar Sin za ta shirya gasar wasannin kwallon tebur da ta fi kyau a tarihi. Sabo da na taba shiga gasani da yawa a kasar Sin, kasar Sin ta shirya gasanni da kyau a ko wane karo. Sabo da haka ne, na yi imani cewa, kasar Sin za ta shirya wata gasar wasan kwallon tebur a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing da ta fi cin nasara a duk tarihin Olympics.'

Mr. Segun Toriola ya fi so 'dan wasan kwallon tebur na kasar Sin Mr. Ma Wenge, amma Madam Bose Kaffo ta fi so Wang Liqin, ta ce, 'Dalilin da nake sonsa shi ne, domin ba ya fasa aikinsa har abada. Yana da karfi, lokacin da nake kallon wasansa, na ji kamar ina kallon Ronaldo ne ke wasan kwallon kafa.'(Danladi)