Ran 21 ga wata, an kammala aikin mika wutar wasannin Olympics na Beijing a birnin Qingdao kirar "birnin jirgin ruwa mai filafili" na lardin Shandong, bayan haka, za a fara mika wutar yola a birnin Linxi tasha ta biyu ta lardin Shandong.
Birnin Linxi yana da mutane mafi yawa da fadin kasa mafi girma a lardin Shandong, tare da dogon tarihi da yawan ala'du.
Bisa labarin da muka samu, an ce, za a fara mika wutar yola a ran 21 ga wata da karfe 5 na yamma daga filin Xiaobudong zuwa filin Phoenix a birnin Linxi, tsawon lokacin mika wutar yola zai kai awa gada da rabi.
|