Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-21 10:12:58    
Shugaban kasar Sin ya kai rangadi zuwa birnin Qingdao na kasar

cri

Jiya 20 ga wata, shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya kai rangadi zuwa birnin Qingdao na lardin Shandong na kasar, don binciken yadda ake share fagen wasan kwale-kwale na Olympic da za a gudanar a birnin, da kuma yin nazari a kan yadda masana'antu ke gudana a halin da ake ciki yanzu.

A matsayinsa na birnin da ke taimakawa wajen gudanar da wasannin Olympics na Beijing, birnin Qingdao na daukar nauyin gudanar da wasan kwale kwale na Olympic. Tun daga tsakiyar watan Yuni da ya wuce, an sami dimbin kainuwa a mashigin tekun birnin Qingdao, kuma sau da dama ne Mr.Hu Jintao ya ba da umurni, inda ya nemi a yade su cikin gaggawa, kuma ya zuwa yanzu, an samu babbar nasara wajen yade kainuwar.

Mr.Hu Jintao ya kuma yi bincike a kan tsarin jagorancin wasan kwale-kwale na Olympic. Ya ce, yau kwana 19 ne kawai ya rage a soma wasannin Olympics, muna fatan za ku share fagen wasan sosai da sosai, don tabbatar da samun cikakkiyar nasarar gudanar da wasan.

Tun farkon shekarar da muke ciki, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa yadda ya kamata kuma cikin sauri, amma kuma yana fuskantar wasu matsaloli, ciki har da raguwar saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya da hauhawar farashin kayayyaki da dai sauransu, wato ke nan yana kara fuskantar babban kalubale. Mr.Hu Jintao ya kuma yi bincike a kan yadda masana'antu na wurin ke gudana. Ya ce, ya kamata a gaggauta gyaran hanyoyin samun cigaban tattalin arziki, don tabbatar da tattalin arziki da ya bunkasa yadda ya kamata kuma cikin sauri.(Lubabatu)