
A ran 18 ga wata da safe, An kammala mika wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Anshan cikin nasara


An yi bikin fara mika wutar a filin Yufoshan na birnin Anshan. Dan wasan harbi na kasar Sin Wang Yifu ya dauki wutar ta farko da aka mika a birnin Anshan. Daga baya, an mika wutar a wurin yawon shakatawa mai suna Yufoshan da filin Gaoxin da filin Huoju da sauran wurare masu ban sha'awa, wurin karshe da aka kai wutar, shi ne kofar makaranta ta farko. Tsawon hanyar da aka bi wajen mika wutar ya kai kilomita 7.8. Yawan jama'ar da suka dauki wutar yola ya kai 175.(Abubakar)
|