Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-18 15:36:27    
Kabilar da ta fi yawan mutane da kabilar da ta fi karancin mutane a kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Alh.Sabo Bawa Bako, wanda ya fito daga jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ya turo mana a kwanan baya, malamin ya ce, muna sa ran za ku ba mu tarihin kabilar da ta fi kowace kabila karancin mutane da kuma kabilar da ta fi kowace kabila yawan mutane a kasar Sin. Zan so samun amsar, in da da hali, ku gabatar da shiri a gidan rediyonmu, domin amfanin dukkan masu sauraro.

Masu sauraro, tun zamanin da, Sin kasa ce da ke da kabilu masu yawa, kuma a halin yanzu, yawan kabilun da ke zaman rayuwa a nan kasar ya kai 56. Ban da kabilar Han, sauran kabilu 55 ana kiransu kananan kabilu sabo da yawan mutanensu ba shi da yawa idan an kwatanta shi da na kabilar Han.

A nan kasar Sin, kabilu daban daban sun dade suna zaman cude-ni-in-cude-ka, wato a wuraren da 'yan kabilar Han suka fi zama, ana iya samun 'yan kananan kabilu, a wuraren da aka fi samun 'yan kananan kabilu kuma, akwai 'yan kabilar Han. Ko da yake kananan kabilun kasar Sin ba su da dimbin jama'a, amma suna barbaje kusan ko ina a makamakan filaye na kasar Sin, musamman ma a Mongoliya ta gida da Xinjiang da Ningxia da Guangxi da Tibet da Yunnan da Guizhou da Qinghai da Sichuan da dai sauran larduna da jihohi na kasar. Daga cikinsu kuma, lardin Yunnan ya kasance lardin da ya fi yawan kabilu a kasar Sin, kuma yawan kabilun da ke zama a wurin ya kai har 25.

Daga cikin kabilu 56 na kasar Sin, kabilar Luoba da ta fi zama a yankin Luoyu da ke kudu maso gabashin Tibet ita ce ta fi kowace kabila karancin mutane a halin yanzu, kuma bisa kidayar jama'a da aka gudanar a shekarar 1990, yawan mutanensu ya kai sama da 2300 ne kawai. 'Yan kabilar Luoba suna da harshensu, amma ba su da rubutu. Sabo da haka, a cikin shekaru da dama, suna yada al'adunsu daga wannan zuriya zuwa wata zuriya ta hanyar wakoki ko tatsuniyoyi. 'Yan kabilar Luoba sun sami tasiri sosai daga 'yan kabilar Tibet a kan al'adunsu, musamman ma a fannin abinci. Suna son cin gasashen nama da busashen nama da tuwon da aka yi da gero, tare kuma da yaji. Sa'an nan, suna son shan giyar da aka yi da masara.

Bayan haka, kabilar da ta fi kowace kabila yawan mutane a kasar Sin ita ce kabilar Han, kuma yawan mutanenta ya kai biliyan 1 da miliyan 42, sabo da haka kuma ta zama kabilar da ta fi yawan mutane har a duk duniya. kakanin kakanin 'yan kabilar Han sun dade suna ayyukan noma, sabo da irin al'adarsu, 'yan kabilar Han sun fi cin hatsi iri iri tare kuma da sauran wasu naman dabbobi da ganyen lambu a zamansu na yau da kullum.

A nan kasar Sin, kabilu daban daban, duk da yawan mutanensu da cigaban tattalin arzikinsu da kuma al'adunsu da addinansu daban daban, daidai suke. Tsarin mulkin kasar Sin ya tanadi cewa, "kabilu daban daban daidai suke a jamhuriyar jama'ar Sin, kuma gwamnati tana tabbatar da hakkokin kananan kabilu, tana kiyaye da kuma bunkasa zaman daidaici da hadin kai da kuma taimakon juna a tsakanin kabilu daban daban, sa'an nan tana hana nuna bambanci ga ko wace kabila ko kuma yi mata danniya."

Gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai da dama wajen tabbatar da hakkokin kananan kabilu daban daban da moriyarsu. Tsarin cin gashin kai a yankunan da kananan kabilu ke zama wata babbar manufa ce da gwamnatin kasar Sin ta dauka bisa hakikanin halin da take ciki, haka kuma wani muhimmin tsarin siyasa ne na kasar. Tsarin cin gashin kansu shi ne a karkashin jagorancin gwamnatin tsakiyar kasar Sin, kafa hukumomi masu zaman kansu a yankunan kananan kabilu, ta yadda kananan kabilu su ne suke tafiyar da harkoki da kansu. A watan Mayu na shekarar 1947, Sin ta kafa yanki mai cin gashin kansa na Mongoliya ta gida, wanda ya kasance irinsa na farko a kasar. Daga baya, bi da bi ne sai aka kafa yankuna masu cin gashin kansu na 'yan kabilar Uygur da na 'yan kabilar Zhuang da 'yan kabilar Hui da kuma 'yan kabilar Tibet. Ya zuwa yanzu dai, daga cikin kananan kabilun kasar Sin 55, akwai 44 da suka kafa yankuna masu cin gashin kansu, kuma fadin yankuna masu cin gashin kansu ya dau kimanin kashi 64% na fadin kasar Sin baki daya.

Masu sauraro, kamar yadda kuka sani, Sin tana aiwatar da shirin kayyade haihuwa. Bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, don neman kyautata ingancin al'ummar kananan kabilu da kuma gaggauta bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma a yankuna masu cin gashin kansu na kananan kabilu, Sin tana kuma aiwatar da shirin kayyade haihuwa a yankuna masu cin gashin kansu na kananan kabilu, Amma duk da haka, ta nuna sassauci ga kananan kabilunta, ta yadda saurin karuwar yawan kananan kabilu ya wuce matsakaicin saurin karuwar al'ummar kasar Sin baki daya.

Ban da wannan, yawancin kananan kabilun kasar Sin suna da harsunansu na kansu, kuma dokokin kasar Sin suna tabbatar da 'yancin kananan kabilu na yin amfani da harshensu da kuma bunkasa shi. Gwamnatin kasar Sin ta kuma kafa sassan nazarin harsunan kananan kabilu, don horar da masana kan harsunan kabilu daban daban da kuma sa kaimi ga bunkasuwar harsunan kananan kabilu.(Lubabatu)