Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-18 15:31:32    
'Yan wasan kasar Kazakhstan na samun kyakkyawan horo don halartar gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, shekarar 2008, shekara ce da kasar Kazakhstan ta halarci gasar wasannin Olympics ta yanayin zafi a karo na biyar. Kwanakin baya ba da dadewa ba, wakilinmu ya bakunci babban sakataren kwamitin wasannin Olympics na kasar Kazakhstan Mr. Timur Dossymbetove don jin ta bakinsa a game da yadda 'yan wasan kasarsa suke himmantuwa wajen samun kyakkyawan horo don halartar gasar wasannin Olympics ta Beijing.

A matsayin babban sakataren kwamitin wasannin Olympics na Kazakhstan, Mr. Timur yakan ja ragamar tawagar wasannin motsa jiki zuwa wurare daban-daban na sauran kasashen duniya don halartar gasanni. Birnin Beijing yana daya daga cikin biranen da ya sha kai ziyara. Mr. Timur ya furta cewa, birnin Almaty ya yi alfaharin zamo zango na farko na zagayawa da fitilar wasannin Olympics a yankin waje da kasar Sin. Lallai yawo da fitilar wasannin da aka yi a wannan gami ta tada himmar al'ummomin kasar ta Kazakhstan wajen sa ran alheri ga gagarumar gasar wasannin Olympics ta Beijing. Mr. Timur ya kuma fadi cewa: "Nakan je Beijing, inda na ganewa idona manyan sauye-sauyen da aka yi kusan shekaru ashirin da suka gabata. Lallai birnin Beijing kara kyakkyawa yake a kowace rana, kuma gwamnatin birnin Beijing ta samu ci gaban a-zo-a-gani a fannin fasahohin bunkasa wasannin motsa jiki na zamani da kuma kirkire-kirkiren harkokin wasannin motsa jiki. A yanzu haka dai, ya kasance da kyakkyawar dangantaka dake tsakanin kasashen Kazakhstan da Sin. Ko shakka babu, mika wutar yola ta wasannin Olympics da aka yi a Kazakhstan zai kara inganta zumuncin dake tsakanin jama'ar kasashen biyu".

Sa'annan Mr. Timur ya buga babban take ga aikin share fagen gasar wasannin Olympics da gwamnatin birnin Beijing take yi. Yana mai cewa: "Na hakkake cewa, gasar wasannin Olympics ta Beijing za ta zama daya daga cikin wasannin Olympics mafi kayatarwa. Wassu gine-ginen wasannin Olympics na Beijng musamman ma fitattun gine-gine guda biyu wato ginin babban filin wasannin motsa jiki na kasar Sin mai siffar gidan tsuntsu wato 'Bird's Nest' da kuma ginin cibiyar ninkaya mai siffar ' Tafkin Wanka' wato ' Water Cube' a Turance na janyo hankulan mutane kwarai da gaske. Kazalika, kauyen 'yan wasa na kusa da filaye da dakunan gasanni. Hakan zai samar da sauki ga 'yan wasan".

Ko kuna sane da cewa, Kasar Kazakhstan har kullum tana kan matsayin wata kasa kakkarfa a fannin wasannin motsa jiki a babban yankin Turai da Asiya tun bayan da ta samu mulkin kanta a shekarar 1991. In ba a manta ba, a gun gasar wasannin Olympiics ta shekarar 2004 a birnin Aden na kasar Girka, kasar ta Kazakhstan ta samu lambar zinariya guda, da lambobin azrufa guda 4 da kuma lambobin tagulla guda 3, wato ke nan ta zo ta 40 a cikin jerin kasashen da suka samu lambobin yabo. A yayin da Mr. Timur yake tabo magana kan gasar wasannin Olympics ta Beijing, ya furta cewa lallai gasar wasannin Olympics ta Beijing na da muhimmancin gaske ga kasar Kazakhstan, wadda take shiga cikin wani muhimmin mataki na ayyukan share fagen shiga wannan gagarumar gasa. Mr. Timur ya kara da cewa:" A yanzu haka dai, muhimmin aikin dake gaban 'yan wasan kasar Kazakhstan shi ne samun karin iznin shiga wassu ayyukan wasannin Olympics na Beijing. Za mu yi iyakacin kokarin shirya wata kungiya dake hake da 'yan wasa 100 don su shiga gasar wasannin Olympics ta Beijing".

A yayin da wakilinmu ya yi tambaya kan shirin kwasar lambobin yabo da 'yan wasan Kazakhstan za su yi, Mr. Timur ya furta cewa: " Ai gaskiya da kyar muke yin hasashen cewa lambobin yabo yawa ne 'yan wasanmu za su kwashe. Kuma muna sa ran za su yi kokarin kwasar lambobin yabo guda 8 zuwa 10 a fannin wasannin daukar nauyi, da dambe, da kokawa, da kuma na harbe-harbe da dai sauransu".(Sani Wang)