Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-17 21:22:37    
Baki daga ketare dake cikin yankin kasar Sin suna iya duba tashoshin internet na kasar Sin dake ketare cikin 'yanci a lokacin wasannin Olympics na Beijing

cri

'Tashoshin internet na kasar Sin suna kasancewa cikin 'yanci. Baki daga ketare dake cikin yankin kasar Sin suna iya duba tashoshin internet na kasar Sin dake ketare cikin 'yanci a lokacin wasannin Olympics na Beijing', kamar yadda mataimakin ministan masana'antu da sadarwa na kasar Sin, Shi Guohua a ranar yau Alhamis a nan Beijing.

Sa'annan Mr. Shi ya ce, kasar Sin na da dokoki kan gudanar da harkokin internet wato ke nan tana yin fatali da nuna abubuwa marasa da'a kan internet kamar yadda kasar Amurka ke yi.

Dadin dadawa, Mr. Shi ya furta cewa, kasar Sin ta samu ci gaba da saurin gaske a shekarun baya a fannin bunkasa sha'anin internet. Kuma yawan mutane masu yin amfani da internet ya kai miliyan dari biyu da ashirin ; Ban da wannan kuma, wadanda suke yin amfani da tashoshin internet na Turanci sun kai miliyan daya da dubu dari tara. ( Sani Wang)