Wakilinmu ya ruwaito mana labarin cewa, 'yan makaranta kimanin 364 na kashin farko daga wuraren da bala'in girgizar kasa ya galaibatar da su na kasar Sin sun sauka a birnin Vladivostok dake bakin tekun a yankin Gabas mai nisa na kasar Rasha yau Alhamis domin samun hutu da jinya.
Jakadan kasar Sin dake Rasha Mr. Liu Guchang da mataimakin wakili mai cikakken iko na Rasha dake yankin da dai sauran manya sun je filin jirgin sama don taryensu.
Jakada Liu ya ce, lamarin zai yi tasiri mai muhimmanci ga inganta huldodin dake tsakanin kasashen Sin da Rasha da kuma kara dankon amincin dake tsakanin jama'ar kasashen biyu zuriya bayan zuriya. ( Sani Wang )
|