Bisa labarin da wakiliyarmu ta ruwaito mana, an ce, yara 919 na kashin farko daga wuraren da bala'in girgizar kasa ya rutsa da su a kasar Sin sun tashi zuwa Rasha domin yin hutu da jinya na tsawon kwanaki 21.
Bisa gayyatar da shugaba Medvechev ya yi musu ne, yara'yan kasa da shekaru 16 da haihuwa da yawansu ya kai 1,570 daga wuraren da bala'in girgizar kasa ya galabaitar da su na kasar Sin suka tafi Rasha domin samun hutu da jinya.
Kafin su tashi, shugaba Hu Jintao ya gana da wakilansu cikin halin arziki jiya da safe a nan Beijing, inda ya kuma jinjina wa gwamnatin Rasha da jama'arta bisa tallafi maras son kai da suka yi wa kasar Sin dake yaki da bala'in girgizar kasa da yin ceto. ( Sani Wang )
|