Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-17 15:00:28    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri

Wata tsohuwa mai kishin wasan Opera. An sami wata tsohohuwa mai farin gashi da ake kiranta Yu Jian wadda take da shekaru 79 da haihuwa a binin Yinchuan,babban birnin jihar Ningxia ta kabilar Hui mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta fi kwarewa wajen yin wasan Opera na Beijing wanda a ciki ta kan shiga burtun "sarkin birai" da ya shahara a cikin dukkan sinawa ko ina a duniya. Yu ta fara koyon wasan opera na Beijing ne yayin da take da shekaru bakwai da haihuwa,ta gabatar da wasan yayin da take da shekaru goma da haihuwa. A cikin shekaru sittin da suka shige, ta gabatar da wasanni na Beijing Opera sama da sittin. Ta kasance 'yar wasan Beijing Opera daya kacal da ta shiga burtun "sarkin birai" a kasar Sin.

'Yan makarantar koleji sun yi aiki domin samun kudi. Xiao Yan,wata budurwa ce da take karatu a wani koleji dake birnin Xining,babban birnin lardin Qinghai ta yi aiki ta samu kudin Sin RMB Yuan sama da dubu yayin da take hutu na yanayin hunturu. 'Yan makaranta kamar Xiao Yan sun yi yawa a birnin Xining da suka yi aiki a lokacin hutu na hunturu,sun gogu daga ayyukan da suka yi haka kuma sun samu kudin karatu da saukaka nauyin da ke bisa wuyan iyalansu. Xiao Yan ta ce "kudin da na samu daga wajen aiki ya iya zama wani kashin kudin makaranta,ya dan rage nauyin da ke bisa wuyan iyayena,ni ma na kara kwarewa a cikin aiki." Xiao Yan ta zo makaranta ne daga wata iyalin manoma da ke fama da talauci.

Wani miji ya ba da lada ga matarsa saboda ta fadi gaskiya.Liu Shugen,wani mazauni ne a birnin Chengdu,babban birnin Sichuan na kasar Sin ya ba matarsa lada na kudin Sin Yuan dari hudu sabo da ta gano wata fartamani a kan titi ba ta sa shi a cikin aljihunta ba. Da matarsa Chen Xiufen ta gano fartamanin dake cike da kudin tsaraba da kuma katin banki a kan titi a ranar laraba da ta shige,ta bude fartamanin ta samo alama mai amfani ta yi cigiyar mai fartamamin,daga baya ta samo shi. Ta ba shi fatamanin.Da ganin haka, mijinta ya ba ta lada ya yi alfaharin abin da matarsa ta aikata.

An ceci wani yaro da ubansa. Kwanan baya an sami wani tsoho mai suna Wang Weiqing mai yawan shekaru 58 da haihuwa ya ceci wani yaron da ya fada a cikin wani karamin tafki dab da wani kauye a gundumar Danyang na lardin Jiangsu dake gabacin kasar Sin.Yaron da ake kiransa Wang Yuhao yana da shekaru bakwia da haihuwa yayin da ya ke wasa dab da karamin tafki ya fada a cikin tafki.Ya yi sa'a a wannan lokaci matafiyi Wang Weiqing na wucewa ya kubutad da shi daga tafkin.Wannan shi ne ba karo na farko ba da Mr Wang Weiqing ya kubutad da mutane daga tafki ba,an ce ya kubutad da mutane hudu daga cikin wannan tafki cikin shekaru na baya.Mr Wang Wiqing ya kuma kubutad da uban yaron Wang Hongwei yau da shekaru sama da ashirin da suka shige.

An kama wani mai satar wayoyin salula. A ranar talata da yamma da ta shige,a birnin Fuzhou,babban birnin lardin Fujian,wasu 'yan makarantar sakandare sun kama wani dan sare. Wata rana wasu 'yan makaranta suna wasan kati a cikin wani shagon sayar da ganyayen ci dab da makarantarsu wani mutum mai matsakaicin shekaru ya zo wajensu ya yi yunkurin satar wayar salula daga daya daga cikinsu.Da ya dauki salula yana neman fita nan take 'yan makaranta sun kama shi sun kai shi gidan 'yan sanda.(Ali)