Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-16 22:09:57    
An kawo karshen yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a yankin Yanbian

cri
A ran 16 ga wata da yamma, an kawo karshen yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a birnin Yanji, hedkwatar yankin Yanbian na kabilar Korea mai cin gashin kai da ke lardin Jilin na kasar Sin.

An kaddamar da aikin yawo da fitilar a filin wasa na jami'ar Yanbian da ke birnin Yanji, kuma a karshe dai an kai fitilar zuwa filin Jindalai. Furen Jindalai fure ne na yankin Yanbian na kabilar Korea mai cin gashin kai, wanda ya alamanta karfin zukatan jama'ar yankin da kishin kasa da suke da shi, a waje daya kuma ya bayyana zaman lafiya da kuma zumunci a tsakanin mutane.

An gudanar da bikin yawo da fitilar har na sa'o'i uku, kuma tsawon hanyar da aka bi ya kai kilomita 7.8, masu yawo da fitilar da yawansu ya kai 188 sun halarci bikin. (Bilkisu)