Tun daga karfe sifiri na ranar 20 ga wata, wasu filayen jiragen sama na kasar Sin ciki har da filin jiragen sama na babban birnin Beijing za su dauki matakan bincike domin tabbatar da tsaro a yayin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics.
A lokacin, hukumomin tsaron zaman lafiyar jama'ar kasar Sin za su kaddamar da na'urorin bincike a wuraren da ake shiga tashoshi masu lambobi 1, da 2, da 3 na filin jiragen sama, dukkan fasinjoji, da mutanen da suka raka su, da kuma ma'aikatan hukumomi daban daban na filin jiragen sama, wato bayan da aka yi musu bincike, sa'an nan kuma za su iya shiga cikin tashoshin jiragen sama.(Danladi)
|