
Ana kokarin sanya baki da su ji dadi a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing, kamar yadda aka tsara takardun abincin Sinawa cikin harshen Turanci, kuma ana saukaka ajandar neman izinin zuwa kasar Sin.
A jajibirin gasar wasannin Olympic ta Beijing, yawan dakunan cin abinci da suke amfani da takardun tsarin abincin Sinawa da aka yi da harshen Turanci yana ta karuwa. An kuma sanya hotunan abinci a kan takarda.

Bisa kididdigar da hukumar tsaron jama'ar birnin Beijing ta yi, an ce, mutanen kasashen waje dubu 86 sun riga sun yi zama a nan birnin Beijing fiye da watanni 6, a waje daya kuma, yawan mutanen da suke dan zama a nan birnin Beijing kasa da watanni 6 ya kai kimanin dubu dari 4, wato ya karu da kashi 40 cikin kashi dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara.
Haka kuma, 'yan jaridun kasashen waje sun gano wasu sauye-sauyen da aka yi a Beijing. Jagoran sashen kamfanin dillancin labaru na Ria-Novosti na kasar Rasha da ke nan Beijing ya ce, za su iya neman labaru kai tsaye, ba kamar a da ba dole ne su nemi izinin neman labaru daga ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin. (Sanusi Chen)
|