Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-16 15:34:20    
An kai ziyara a manyan farfajiyoyin Lardin Shanxi

cri

A cikin shirinmu na yau za mu raka ku zuwa manyan farfajiyoyin Lardin Shanxi . Galibin manyan farfajiyoyin Shanxi wasu farfajiyoyi ne masu zurfi . Suna da sauki kuma suna cikin halin karimci . Galibinsu an gina su a lokacin Daular Ming da Daular Qing ta kasar Sin .

Ko da ya ke sun sha iska cikin shekaru daruruka , amma har ila yau sun jawo hankulan mutane sosai . Babbar farfajiyar iyalin Qiao dake tsakiyar Lardin Shanxi daya ce wadda ta fi kasance da wakilci daga cikin manyan farfajiyoyi .

Daga waje ma iya ganin cewar , babbar farfajiyar iyalin Qiao tana da bango mai kauri . Bakaken gidaje suna kewayan farfajiyar . Sabo da haka tana da 'kayantarwa sosai . Da ka shiga cikin babbar farfajiyar , wata hanyar dutse mai tsawon mita 80 ta raba kashi na kudu da na arewa . Kowane kashi kuma yana da kananan farfajiyoyi guda uku . A karshen hanyar akwai Gidan tsafi wanda 'yan iyalin Qiao suke bauta kakaninsu . Gidan tsafi yana fuskantar babbar kofar farfajiyar da nisa .

Babbar farfajiyar wadda take da kananan farfajiyoyi 6 a kudu da arewa tana da fadin muraba'in kusa mita dubu 9 . Malam Yang Guang mai yawon shakatawa wanda ya zo daga lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin ya jiku kwarai da gaske . Ya ce ,

A da ban taba ganin gidajen kwana dake arewacin kasar Sin ba . Karo na farko ne na shiga cikin babbar farfajiyar. Launin wadannan gine-ginen farfajiyar yana da kyaun gani . Launi mai

tushe na farfajiyar toka ne . Sa'an nan kuma an gina dakuna masu launin ja da ba'ki . Wannan ya dace da bukatar mutane na zamani . A wajen zayyana an mai da hankali mai tsanaki . A tsakiya kuma an yi wasu sauye-sauye . Sabo da haka farfajiyar tana da halin karinci sosai .

A tsohuwar farfajiyar iyalin Qiao an gina gorar dutse don daure dawaki . Da keken doki da kujerun dauka mutane suna fitowa da shigowa , sun sami sauki daga gorar dutse .

Idan za ka yi yawon shakatawa a wannan farfajiyar , to , za a ba ka mamaki a dakunan kwana masu yawa . An zaune da su a matsayi daban daban cikin adalci . Tubali da marufi , itace da dutse , duk kayan da aka yi amfani da su sun bayyana kwararrun fasahohi na masu gina farfajiyar . Wu Liangyong wanda yake nazarin fasahohin gine-gine yana ganin cewa , babbar farfajiyar iyalin Qiao abu mafi kyau ne na ginin mazaunan arewacin kasar Sin .

Kayayyakin da aka yi amfani da su a wajen kyautata farfajiyar iyalin Qiao galibinsu katako ne da tubalai. An sa kofofi da banguna da su ci ado da tubalan musamman wadanda aka yi sassakar abubuwa masu faranta rai .

Lokacin da aka kyautata farfajiyar , masu gine-ginen su kan mai da hankali a kan kofa da taga . Kamar yadda idon mutane yake , sun nuna fifiko ga kofofi da tagogi.

An fara gina babbar farfajiyar Qiao ne a lokacin tsakayar karni na 18 . Bayan haka a cikin shekaru fiye da 200 , an yi ta yi habakawa kuma an kashe kudin azurfa dubu dubai , shi ya sa ta zama farfajiyar yau . Yanzu babbar farfajiyar tana da dakuna fiye da 300 . Kayayyakin da ake ajiye a cikin dakunan suna da daraja sosai . Ciki har da madubi mai kyau wanda aka kera a kudancin Asiya . Akwai agogo mai kyakkyawa wanda ya zo daga kasar yamma . A cikin lambun shan iska na iyalin Qiao akwai furani da duwatsu masu ban mamaki wadanda aka jigilar da su daga kudancin kasar Sin.