A ran 12 ga wata, an samu girgizar kasa mai karfin digiri 8.0 na ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, haka kuma birane da larduna fiye da 10 na kasar Sin da kuma kasashen Vietnam da Thailand sun samu girgizar kasa bisa matsayi daban daban.
Sun Shihong, shi ne babban mai ba da rahoto na cibiyar girgizar kasa ta kasar Sin, kuma ya dade yana gudanar da ayyukan nazarin girgzar kasa har shekaru gomai. Ya bayyana cewa, dalilin da ya sa kasar Sin ba ta yi hasashe sosai kan wannan girgizar kasa ba shi ne sabo da a cikin dogon lokacin kafin aukuwar girgizar kasa, ba a gano harkokin girgirzar kasa da ke da babban matsayi a wurin da ke cibiyar girgizar kasa da kuma yankuan da ke kewayensa ba, a waje daya kuma ba a samu al'amun girgizar kasar da tabbas na tafe ba. Kuma ya kara da cewa,
"Idan ana son yin hasashen mummunar girgizar kasa kamar wannan karo a cikin gajeren lokaci, to kullum a kan dogaro da abubuwa biyu, na farko shi ne dabbobi suna tafiyar da harkokinsu ba kamar kullum ba, na biyu shi ne an samu alamomi kafin aukuwar girgizar kasa, kamar faruwar kananna girgizar kasa kullum. Amma a wannan karo ba a samu harkokin da su kan auku kafin girgizar kasa ba, haka kuma ba a gano harkokin da ba na kullum ba da dimbin dabbobi suka tafiyar. Sabo da haka ba a yi hasashe kan girgizar kasa ba."
A hakika dai, kasa yin hasashen girgizar kasa da za ta auku ba da jimawa ba ba wata matsala ce ta kimiyya a gaban kasar Sin kawai ba. Yanzu kasashe daban daban suna yin nazari kan hasashen girgizar kasa, dabarun kimiyya sun yi kadan a wannan fanni.
To, wace matsala ce ake gamuwa wajen hasashen girgizar kasa? Chen Jianmin, shugban hukumar kula da girgizar kasa ta kasar Sin ya bayyana cewa, girgizar kasa ta kan auku a wuraren da nisansu ya kai kilomita 15 da doron kasa. Kuma ya kara da cewa,
"Girgizar kasa ta kan auku a wuri mai zurfi sosai da ke karkashin doron kasa. Kuma a kan yi hasashen girgizar kasa ta hanyar dudduba da binciken wuraren da ke karkashin kasa, amma yanzu dan Adam bai samu bunkasuwa sosai a wannan fanni ba. Kasar Sin ta haka wata rijiya wajen dudduba girgizar kasa, amma tsayinta ya kai kilomita 5 kawai a karkashin kasa."
Haka kuma Sun Shihong, mai ba da rahoto na farko na cibiyar girgizar kasa ta kasar Sin ya gaya wa wakilinmu cewa, bambancin tsarin doron kasa tsakanin wurare daban daban ya kayyade labarun da aka tattara wajen binciken girgizar kasa bisa wani matsayi, ta haka an kara wahalolin da aka sha wajen hasashen girgizar kasa. Kuma ya kara da cewa,
"Alal misali, game da girgizar kasa mai karfin digiri 5 da ta auku a gabashi da kuma yammacin kasar Sin, kullum sun sha bamban a fannin salonta. Haka kuma harkokin da ba na kullum ba da suka faru a cikin ko wace girgizar kasa sun sha bamban, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da bambancin da ke tsakanin wurare da kuma karfin girgizar kasa."
Ko da haka, amma bisa kokarin da aka yi a cikin dimbin shekarun da suka gabata, kasar Sin da sauran kasashe sun tattara labaru masu dimbin yawa game da girgizar kasa, kuma sun samu babban ci gaba wajen hasashen girgizar kasa da za su faru a cikin matsakaici da kuma dogon lokaci. A waje daya kuma masu ilmin kimiyya sun kara fahimtar cewa, wahalolin da suka sha wajen yin hasashen girgizar kasa da za ta faru a cikin gajeren lokaci sun saba da wadanda suke tsammani.(Kande Gao)
|