Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-16 15:21:45    
Sin na kara kulawa da aikin harhada maganin sa kuzari domin wasannin Olympics na Beijing

cri

Aminai 'yan Afrika, kwanan baya bada dadewa ba, a nan birnin Beijing, wani jami'in da abin ya shafa na sashen sa ido kan ingancin kayan abinci da na magunguna na kasar Sin ya furta cewa, ko yake gasar wasannin Olympics na karatowa, shi ya sa gwamnatin kasar Sin take sanya kokari matuka wajen kulawa da ayyukan harhada maganin sa kuzari da na saye da sayarwa da zummar kirkiro wani kyakkyawan muhalli na gudanar da gasannin Olympics bisa matsayin daidaici a nan Beijing.

Ko kuna sane da cewa, bullowar maganin sa kuzari takan janyo cikas ga tarurrukan wasannin Olympics da aka gudanar a da. Tun bayan da gwamnatin birnin Beijing ta samu iznin shirya gasar wasannin Olympics ta 29 a shekarar 2001, gwamnatin kasar Sin ta dauki jerin matakai masu amfani na kara sa ido kan maganin sa kuzari da zummar kirkiro wani kyakkyawan muhalli na gudanar da gasannin Olympics na Beijing bisa daidaici. Tuni a shekarar 2004, gwamnatin kasar Sin ta fito da " Ka'idoji kan aikin kulawa da maganin sa kuzari". Hakan ya samar da abun dogaro ta fuskar shari'a ga kara kulawa da maganin sa kuzari. Ban da wannan kuma, tun daga karshen rabin shekarar da ta gabata, sassan sa ido kan ingancin magunguna, da bangarorin masana'antu da kasuwanci da kuma ma'aikatun tsaron zaman lafiya da dai sauransu na kasar Sin sun kuma hada kansu wajen gudanar da bincike musamman kan maganin sa kuzari bisa babban sikeli a dukkan fadin kasar yayin da suke kara kulawa da ayyukan harhada magungunan sa kuzari da na saye da sayarwarsu domin tabbatar da kasancewar magungunan sa kuzari a matsayin magungunan ceton rayukan 'yan wasa maimakon wani kayan aiki da suke yin amfani da shi wajen yin magudi.

Mista Wu Zhen, mataimakin shugaban hukumar kula da ingancin kayan abinci da magunguna ta kasar Sin ta bayyana cewa, sassan da abin ya shafa na kasar Sin sukan girke ma'aikata masu sa ido zuwa ga wassu masana'antun harhada magungunan sa kuzari domin gudanar da bincike cikin sirri a game da ayyukan harhada magundunan da na saye da sayarwarsu; Sa'annan ana bukatar rubuta kalmomin fadakar da 'yan wasa don kada su yi kuskuren shan magungunan dake kunshe da kwayoyin magungunan sa kuzari. Mista Wu ya furta cewa: " Lallai kasar Sin ta samu sakamako mai gamsarwa a fannin kulawa da maganin sa kuzari. Ban da wannan kuma, a tsakiyar watan Mayu na shekarar da muke ciki, hukumar sa ido kan ingancin kayan abinci da magunguna ta kasar Sin ta shirya wasssu kungiyoyin aiki zuwa birane shida wato birnin Beijing, babban mai masaukin gasar wasannin Olympics da sauran birane guda biyar wato Tianjin, da Shenyang, da Qingdao, da Qinhuangdao da kuma Shanghai wadanda suke bada hadin gwiwa wajen shirya gagarumar gasar domin gudanar da bincike cikin sirri daga dukkan fannoni. Sakamakon binciken ya shaida cewa, a galibi dai, masana'antun harhada magunguna da kamfanonin sayar da kayayyakin sari na magungunan da kuma kantunan sayar da kayayyakin koli na magungunan sun cimma bukatun da ake da su na sa ido kan magungunan sa kuzari."

Kazalika, Mista Wu Zhen ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da ma'aunonin yanke hukunci mai tsanani kan wadanda suka karya dokoki a game da maganin sa kuzari duk da cewa ta kan gamu da wassu matsaloli. Wassu mutanen da suka karya dokoki sukan yi amfani da internet na ketare domin sayar da maganin sa kuzari.Mista Wu ya kara da cewa: "Lallai ana bukatar hadin gwiwa da goyon baya daga gamayyar kasa da kasa da kuma kasashe daban-daban na duniya domin batun yaki da maganin sa kuzari wani batu ne dake kalubalantar dukkan kasashen duniya. Muna so mu yi kokari tare da gamayyar kasa da kasa wajen kara yaki da maganin sa kuzari, ta yadda za a kiyaye wani kyakkyawan muhalli na gudanar da gasannin Olympics bisa daidaici". ( Sani Wang)