Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-16 15:12:47    
Wani labarin da ya shafi zaman rayuwar wani nakasashe mawaki mai suna Liang Fuping

cri

A birnin Chongqing da ke kan tsaunuka a kudu maso yammacin kasar Sin , akwai wani namijin da kusan kowa ya san shi, yana da makogwaro mai iya fitar da murya mai dadin ji. Ba ma kawai ya iya rera wakoki ba, hatta ma ya iya rubuta wakoki. Amma saboda ya zama nakasasshe bisa sakamakon kamuwar ciwon kafa, shi ya sa ya sha wahaloli da yawa wajen tafiya da sandan guragu tare da kayan kidan da ake cewar "guitar". Ya halarci gasar rera wakoki iri iri da yawa, har ma ya fitar da kundin wakokinsa. Kodayake ya fuskanci wahaloli da yawa wajen zaman rayuwa, amma ya kan cewar ba kome! Sunan namijin din shi ne Liang Fuping.

Gidan Laing Fuping yana wani titin da ake kira "Nanpingzhengjie" na birnin Chongqing.An haife shi a shekarar 1963 a wani gidan da ke bakin kogin Jialingjiang na birnin Chongqing, mahaifiyarsa masakiya ce, kuma tana kan kwanta a kan gado bisa sakamakon kamuwar ciwace-ciwace cikin dogon lokaci, mahaifinsa yana aiki a wani sashen hanyar jiragen kasa, babansa bai iya kula da gidansu yadda ya kamata ba saboda ayyuka na da yawa gare shi, lokacin da Mr Liang fuping ya cika shekaru 2 da haihuwa , ya kamu da ciwo a kan kafarsa, kai, abin nan ya kara wahaloli ga mutanen gidansu , ya ce, tun lokacin da nake karami, ban iya yin wasa tamkar yadda sauran abokan wasa suka yi ba, sai na yi wasa da wake-wake. Ya ce, tun lokacin da nake karami, ina son rera wakoki sosai da sosai. Lokacin da nake saurarar wata waka, sai na yi tunani da cewa, me ya sa an rubuta wakar tamkar hakan nan? Ina dalilin da ya sa wakar tana da dadin ji sosai? Mutane da yawa ba su iya yin irin tunani ba, amma ni kadai na iya yi sosai.

Mr Liang Fuping ya koyi ilmin wake-wake ba tare da bata lokaci ba . Ilmin wake-wake da ya samu a karo na farko daga ajin koyar da ilmin wake-wake na makaranta ne, da farko a gidansa kawai yake gwajin rera wakoki, sa'anan kuma ya yi gwajin rera wakoki a bakin kogi, a kowace rana, yana gwajin rera wakoki cikin sa'o'I biyu ba tare da kasala ba.

Diyarsa ta ce, tun da nake karama, ina girmamawar babana sosai, duk saboda halinsa na rashin tsoron wahaloli tare da nuna yawan hakuri . Kannensa ya ce,a wancan lokaci, na yi masa rakiya sosai, a yanayin zafi, mun yi wanka a cikin kogi, sai ya rera wakoki a bakin kogin, in ana ruwan sama, to na bude masa laima , na goye da wana, har wa yau dai na raka shi ba tare da kasala ba.

Aurensa na farko ya mutu bisa sakamakon fama da talauci sosai, sa'anan kuma ya gamu da wata budurwa mai suna A Jiao kuma mai jin tausayi. A idon A Jiao, ciwon kafar Liang Fuping ba katangar da aka gitta a tsakaninta da Mr Liang ba, A Jiao tana son wakokinsa, kuma tana son kwarewarsa ta rera wakoki da kuma faranta rai da ya yi a zaman rayuwa, ta bayyana cewa, da farko, wakarsa tana jawo sha'awata sosai da sosai, na biyu, shi mutum ne mai jin tausayi sosai, ya kula da babana sosai da sosai, a kowace rana muna farin ciki sosai duk saboda zukatanmu sun hadu gu daya.

A shekarar 2007, Mr Liang Fuping ya sami sabon sakamako , wato a watan Disamba na shekarar, ya bayar da kundin wakokinsa a duk fadin kasar Sin.

Mr Liang ya bayyana cewa, abubuwan da ke cikin wakar "kafadar Namiji" da ya rera sun bayyana abubuwan da na ke tsammani a cikin zuciyata, wakar ta bayyana zaman rayuwata sosai da sosai.(Halima)