Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-16 14:41:11    
Don me gwamnatin Sudan ta nuna adawa da tuhumar da kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya ta yi wa shugaban Sudan

cri
A ran 14 ga wata, Luis Moreno-Ocampo, mai gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya dake birnin Hague na kasar Holland ya yi wa shugaban Sudan Omar Al-Bashir tuhuma bisa laifin tada yaki a yankin Darfur na kasar Sudan, kuma ya nemi kotu da ta gabatar da umurnin cafke Omar al-Bashir. Game da wannan batun, Gwamnatin Sudan ta nuna adawa da shi, tana ganin cewa, wannan batu zai lalata yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar Sudan, kuma mai yiwuwa ne zai haddasa rikicin zubar da jini a yankin Darfur. Masu nazari suna ganin cewa, gwamnatin Sudan ta dauki wannan ra'ayi ne bisa manyan dalilai 2:

Na farko, gwamnatin Sudan ba ta amince da tuhumar da kotun hukunta manyan larfuffuka ta duniya ta yi wa Mr. Bashir, ta ce, batun Darfur harkokin gida ne na kasar Sudan, tuhumar da kotun ta yi tana da burin siyasa, wato sa baki cikin harkokin gida na Sudan. Aikin da kotun ta yi zai mai da batun Darfur zama batun duk duniya, gwamnatin Sudan ta nuna adawa da shi a kullum.

Na biyu, gwamnatin Sudan tana ganin cewa, kasar Sudan ba kasar da ta kulla yarjejeniyar Roma ta kafa kotun hukunta manyan laiffuffuka ta duniya ba ce, wannan kotun ba ta da ikon gudanar da ayyukan shari'a kan jama'ar Sudan, shi ya sa, gwamnatin Sudan ba za ta aiwatar da kowane kudurin da wannan kotun ta yi ba.

Bayan da kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya ta yi wa Omar al-Bashir tuhuma, gamayyar kasa da kasa sun mai da martani gare shi. Babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya bayar da sanarwa cewa, ya damu da tuhumar da mai ba da kara na wannan kotu ya yi, domin wannan zai kawo cikas mai tsanani ga ayyukan kiyaye zaman lafiya. Wasu kasashen larabawa da na Afrika da kuma kungiyar taron Musulmi su ma sun ja kunnen kotun domin mugun sakamakon da za ta kawo. Tarayyar kasashen larabawa ta furta cewa, za ta yi shawarwari kan rikicin Sudan. Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Liu Jianchao ya nuna cewa, kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan wannan batun, yana fatan bangarori daban daban da abin ya shafa za su daidaita batun ta hanyar yin shawarwari. Shugaban kasar Amurka Bush ya bayar da jawabi a ran 15 ga wata, inda ya jaddada cewa, MDD tana taka muhimmiyar rawa a kan batun Darfur, ya yi kira ga MDD da gwamnatin Sudan da su kara hadin gwiwa wajen aikin tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa yankin Darfur.

Yanzu, hadaddiyar rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD da tarayyar kasashen Afrika tana gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya a yankin Darfur, rundunar sojoji ta taka rawa wajen kwantar da hankali a yankin Darfur, amma ta fuskanci wasu wahalhalu na karancin sojoji da kudade da guzuri.

Babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya bayar da sanarwa bayan aukuwar batun cewa, yana fatan shugaba Omar al-Bashir ya yi hakuri, kuma ya jaddada cewa, matsayin da MDD ta dauka kan batun Darfur bai sauya ba.

Masu nazari suna ganin cewa, aikin da kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya ta yi ba zai kawo moriya ga aikin daidaita batun Darfur ba, amma mai yiwuwa ne, zai tsananta batun Darfur. Yanzu, akwai dalilai guda biyu da suka sa a kasa samun cigaba a yunkurin bunkasa siyasa a yankin Darfur, na farko, kungiyoyin adawa da gwamnati na wurin ba su son su koma teburin shawarwari; na biyu, wasu kungiyoyin kasashen waje dake da nasaba da wadannan kungiyoyi suna son su nemi moriyar kansu ta hanyar yin amfani da rikicin.

Masu nazari sun nuna cewa, yanzu, ya kamata a daidaita batun Darfur ta hanyar daukaka cigaban kiyaye zaman lafiya da yunkurin bunkasa siyasa gu daya, a waje daya kuma, ba a iya kyale bunkasuwar tattalin arzikin yankin Darfur ba, wannan babbar hanya ce ta daidaita batun Darfur.