Ran 15 ga wata, mun sami labari daga hukumar kula da harkokin dudduba ingancin kayayyaki da sanya ido da binciken cututtuka ta kasar Sin da cewa, a kwanan baya, cibiyar sa ido kan binciken ingancin na'urorin wasannin motsa jiki ta kasar Sin ta kammala binciken ingancin na'urorin wasan lankwashe jiki da za a yi amfani da su a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing.
Mun sami labari cewa, an yi bincike kan filin wasan lankwashe jiki mai fadin murabba'in mita dubu 3 da na'urorin da za a yi amfani da su a cikin shirin wasan tsalle a kan roba wato Trampoline da dai sauransu a wannan karo. Masu bincike sun yi bincike a tsanake a kan kafet da aka shimfida da kushin da 'yan wasa za su fada a kai domin tabbatar da ganin na'urori da filin wasan lankwashe jiki suna da inganci sosai kuma babu abubuwa masu tsini a ciki.
Sa'an nan kuma, bisa ajandar gasa da aka tsara, bayan gasar wasan lankwashe jiki, tilas ne a canza wannan dakin wasan lankwashe jiki zuwa dakin wasan kwallon hannu cikin awoyi 17. A sakamakon kokarin da bangarorin suka yi cikin hadin gwiwa, masanan cibiyar sun amince da shirin da ke shafar matakan wargazawa da muhimman ayyuka da lokaci da kuma ma'aikata.(Tasallah)
|