A albarkarcin begen zuwan wasannin Olympics da Sinawa na dukkan fadin duniya ke yi, tun daga jiya ne aka gudanar da harkar ' Marabtar zuwan wasannin Olympics da kuma samun kyakkyawan tsaro' a babban ofishin kansila na kasar Sin dake birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu.
Kansila Fang Li ya furta cewa, ofishin kansila zai gudanar da wassu gagaruman bukukuwa a ran 2 da kuma ran 8 ga wata mai kamawa domin taya murnar bude gasar wasannin Olympics ta Beijing. ( Sani Wang ).
|