Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-15 20:38:09    
Kasar Sin ta samu taimakon kudi da na kayayyakin da darajarsu ta wuce yuan biliyan 57.4 daga bangarori daban daban na gida da na waje

cri

Ya zuwa ranar 14 ga wata da karfe 12, kasar Sin ta samu taimakon kudi da na kayayyakin da darajarsu ta wuce yuan biliyan 57.4 daga bangarori daban daban na gida da na waje.

Bisa rahoton da ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta bayar an ce, ya zuwa ranar 15 ga wata da karfe 12, mutane 69,197 ne suka rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa da aka samu a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, yayin da mutane 374,176 suka ji rauni, kuma mutane 18,263 suka bace.

Bayan haka kuma, ya zuwa ranar 14 ga wata da karfe 12, gwamnatoci bisa matakai daban daban na kasar Sin sun bayar da kudin Sin yuan fiye da biliyan 59 kan ayyukan yaki da bala'in girgizar kasa, da kuma yin ceto. (Bilkisu)