Bala'in girgizar kasa da ya auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan ta kasar Sin ya riga ya wuce watanni 2. Yanzu ana aikin sake raya yankuna masu fama da bala'in daga dukkan fannoni a nan kasar Sin. A gun wani taron tattaunawa game da aikin sake raya yankuna masu fama da bala'in da gwamnatin kasar Sin da hukumomin majalisar dinkin duniya da ke nan kasar Sin suka shirya a ran 14 ga watan Yuli a nan birnin Beijing, jami'an kasar Sin sun bayyana cewa, kasar Sin tana maraba da al'ummomin kasa da kasa da su shiga aikin sake raya yankuna masu fama da bala'in.
A gun taron, Mr. John Leigh, wani kwararre na hukumar raya kasashen duniya ta kasar Britaniya ya yaba wa kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi wajen fama da bala'in. Ya ce, "Idan an kwatanta ta da sauran kasashe masu tasowa, za a iya gane cewa, gwamnatin kasar Sin ta soma yin fama da bala'in cikin sauri sosai, kuma ta yi aikin ceto da sake raya yankuna masu fama da bala'in da wurwuri. Wannan ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana sauke nauyin siyasa da ke bisa wuyanta da niyyarta ta yin ceto kamar yadda ya kamata."
Wasu jami'an da suka zo daga lardunan Sichuan da Shaanxi da Gansu inda aka samu bala'in girgizar kasa sun kuma halarci wannan taro. Mr. Huang Xulin, wani jami'in hukumar kasuwanci ta lardin Shaanxi ya bayyana cewa, yanzu lardin Shaanxi yana tsara shirin sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa. Lardin Shaanxi yana son koyon fasahohin zamani daga kasashen waje kan yadda za a tsara wani shirin sake raya yankuna masu fama da bala'in. Mr. Huang ya ce, "Yanzu lardin Shaanxi yana tsara shirin sake raya yankuna masu fama da bala'in. An gayyaci dimbin kwararru da masana wadanda suka kware sosai kan aikin sake raya yankuna masu fama da bala'in da su halarci wannan taro. Sauran kasashen duniya suna da kyawawan fasahohin sake raya yankuna masu fama da bala'in. Irin wadannan fasahohin zamani za su iya ba mu jagoranci ga ayyukan tsara da aiwatar da shirin sake raya yankuna masu fama da bala'in."
A waje daya kuma, a gun taron, madam Qiu Hong, mataimakiyar ministan kasuwancin kasar Sin ta nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan yadda za a sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa. Bayan kwanaki 25 da aukuwar bala'in girgizar kasa na Wenchuan, gwamnatin kasar Sin ta bayar da "ka'idojin sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa na Wenchuan". Sannan kuma ta fitar da "daftarin tsara shirin sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa na kasar Sin" da "ra'ayoyin ba da jagoranci kan yadda za a yi aikin sake raya yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa na Wenchuan" daya bayan daya. A cikin wadannan takardun gwamnati, a fili ne aka bayar da tunanin jagoranci da manyan ka'idoji da muhimmin nauyi kan yadda za a yi aikin sake raya yankuna masu fama da bala'in girigzar kasa. Madam Qiu Hong ta bayyana cewa, "Ko shakka babu gwamnati da jama'ar kasar Sin za su dukufa ka'in da ni'in kan ayyukan sake fama da bala'in girgizar kasa. Kuma za su dogara da kansu kan wannan aiki. A waje daya kuma, kasar Sin tana maraba da sauran kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa da su shiga wannan aiki. Musamman za su iya taka rawarsu wajen neman kudade da kyautata karfin yin aiki da tafiyar da harkokin jama'a da suke kwarewa, kuma za su iya nuna goyon baya da taimako ga kasar Sin wajen sake raya yankuna masu fama da bala'in."
A 'yan kwanakin nan da suka gabata, lokacin da yake ganawa da bakin kasar Amurka, Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya kuma bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan matsayin bin manufofin sanya bil Adam a gaban kome da bude kofarta ga kasashen duniya a lokacin da take fama da bala'in girgizar kasa. (Sanusi Chen)
|