Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-15 16:48:24    
An shawo kan matsalar bullar kainuwa a tekun Qingdao, an mayar da haddin ruwa ya koma yadda ya kamata

cri

Yanzu, an riga an shawo kan matsalar bullar kainuwa a tekun Qingdao, wadda ta fito daga tsakiyar tekun Huanghai tun daga karshen watan Mayu na bana, ya zuwa ranar 14 ga wata da yamma da karfe uku, a hakika dai an kwashe kainuwar da ke haddin ruwa da za a shirya gasar tseren kwale-kwale ta wasannin Olympics na Beijing, haka kuma an mayar da haddin ruwa ya koma yadda ya kamata.

Yanzu, an kawo karshen aikin gina shingaye na musamman mai tsawon mita dubu 30 a kewayen haddin ruwa da ke da muraba'in kilomita 50 da za a shirya gasar tseren kwale-kwale ta wasannin Olympics, don hana shigowar kainuwa. A ranar 14 ga wata kuma, kungiyoyin 'yan wasa daga kasashe da shiyyoyi sama da 30 sun soma horo a nan. (Bilkisu)