Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-15 16:12:27    
Beijing ya fara watsa labarai game da ingancin iska da Sinanci tare da Turanci domin gasar wasannin Olympics

cri

Tun daga ranar 14 ga wata, birnin Beijing ya fara watsa labarai game da ingancin iska ta gasar wasannin Olympics da Sinanci tare da Turanci a ko wace rana, a karo na farko ne, za a bayar da rahotanni game da hayakin sulfur dioxide, da nitrogen dioxide, da kuma kura da jama'a suke shaka, bisa abubuwa da hukumar gasar wasannin Olympics ta duniya ta amince da su.

Tun daga ranar 14 ga wata zuwa karshen gasar wasannin Olympics, jama'a suna iya dudduba ingancin iska a tashar internet ta hukumar kare muhalli ta birnin Beijing, wato bjepb.gov.cn.

Birnin Beijing yana watsa dukkan labarai game da ingancin iska ta gasar wasannin Olmpics da Sinanci tare da Turanci, haka kuma yana bayar da rahotanni game da sakamakon da dukkan tashoshin bincike 27 na birnin Beijing suka samu. Jama'a suna iya yin amfani da tashar internet, domin dudduba ingancin iska a wuraren da ke kewayen filaye da dakunan gasar wasannin Olympics da kuma yankunan da suke zama.(Danladi)