Ma'aikatar tarbiyya da kimiyya ta Rasha ta furta a ran 14 ga wata cewa, yara fiye da 900 na yankunan dake fama da bala'in girgizar kasa na kasar Sin za su samu warkewa a yanayin zafi na wannan shekara a hukumomin ba da jiyya ga yara na kasar Rasha.
Hukumomi 6 na ba da jiyya ga yara na Rasha za su karbi yara na yankunan dake fama da bala'in girgizar kasa na kasar Sin daga ran 17 ga wata. Tsawon lokacin da aka yi musu jiyya zai kai kwanaki 21. Ma'aikatar tarbiyya da kimiyya ta Rasha ta bayyana cewa, wadannan yara za su samu jiyya wajen jikunansu da zukatansu.
Kazalika, ma'aikatar tarbiyya da kimiyya ta ce, yaran da suka ji rauni a batun ta'addanci na Beslan na Rasha sun taba samun hidimomin jiyya a kasar Sin, ya kamata Rasha ta ba da tallafi ga yaran yankunan dake fama da bala'in na kasar Sin.(Lami)
|