Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-15 12:13:27    
Ya kamata a gudanar da gasar wasannin Olympics cikin tsimi kuma ba tare da almubazzranci ba, in ji He Guoqiang

cri

Yayin da zaunannen memban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne sakataren kwamitin ladabtarwa na gwamnatin tsakiya ta kasar Sin He Guoqiang ke binciken aikin gina dakuna da filayen gasar wasannin Olympics da kauyen Olympics jiya 14 ga wata, ya bayyana cewar, kamata ya yi sassan sa ido kan gasar wasannin Olympics a matakai daban-daban su sauke nauyin dake bisa wuyansu a tsanake, domin tabbatar da cimma burin gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing cikin tsimi kuma ba tare da almubazzaranci ba.

He Guoqiang ya ce, tare da karatowar gasar wasannin Olympics, ya kamata a cigaba da sa ido kan ingancin dakuna da filaye na gasar wasannin Olympics. A gabannin bikin kaddamar da gasar wasannin Olympics ta Beijing, kamata ya yi a sake gudanar da bincike kan ingancin dakuna da filayen gasar wasannin Olympics, domin bada cikakken tabbacin gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing yadda ya kamata. Kazalika kuma, ya kamata a cigaba da sa ido da binciken aikin yin amfani da kudaden gasar wasannin Olympics, a wani yunkurin bada tabbaci ga yin amfani da kudaden gina dakuna da filayen gasar wasannin Olympics da kudaden gudanar da gasar wasannin Olympics yadda ya kamata kuma daidai bisa ka'idoji da dokoki. A waje daya kuma, He Guoqiang ya ce, ya kamata a bada tabbaci ga gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing, da gasar wasannin Olympics ta nakasassu tare da cikakkiyar nasara, domin gamsar da gamayyar kasa da kasa, da 'yan wasan motsa jiki na kasashen duniya daban-daban, tare kuma da daukacin jama'ar kasar Sin.(Murtala)