Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-15 10:55:22    
Kafofin yada labaru na kasar Nijeriya suna ganin cewa Sin da Rasha da Amurka za su zama kasashen da suka fi samun lambobin yabo na zinariya a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri
Ran 14 ga wata, shafin wasannin motsa jiki na jaridar Guardian wadda ta fi buzuwa ta farko a kasar Nijeriya, ya bayar da wani bayani cewa, kasashen Sin da Rasha da Amurka za su zama kasashen da suka fi samun lambobin yabo na zinariya a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing.

A cikin bayanin, an bayyana cewa, a matsayinta na kasar da za ta karbi bakuncin gasar wasannin Olympic na wannan gami, ba shakka, kasar Sin za ta zama kasar da ta fi samun lambobin yabo na zinariya mafiya yawa, amma idan tana so ta lashe kasashen Rasha da Amurka, don zama lambawan, sai dole ne kungiyar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ta cimma duk nasara a gun gasar wasannin kwallon tebur da gasar wasannin lankwashe-lankwashen jiki da gasar wasannin tsunduma cikin ruwa watau wasannin da Sin ta yi gwaninta, bugu da kari kuma, gasar wasannin kwale-kwale ta kasar Sin ta sami cigaba sosai, ya kamata ta ci nasara a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing. A cikin bayanin, an kimanta cewa, idan Liu Xiang ya iya lashe 'dan wasan kasar Cuba Darron Robles, watakila zai zama dan wasanni ne kawai wanda ya sami lambar zinariya a gun gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle.

Amma a cikin wannan bayani, an yi gargadi ga kasar Sin cewa, bai kamata kasar Sin ta ji murna sosai ba, sabo da kasar Amurka ta gwanance wajen wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da wasannin iyo watau wasannin da suka fi samun lambobin yabo na zinariya.

Dadin dadawa kuma, a cikin bayanin, an bayyana cewa, kasar Rasha ta kasance wata kungiyar wasannin motsa jiki da bai kamata mu nuna bijirewa gare su ba.

A karshe dai, an bayyana cewa, burin da kasar Sin ta saka a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing ba wai kasancewa kasar da za ta sami lambobin yabo na zinariya mafiya yawa ba. haka kuma bayani ya ruwaito maganar da mai ba da taimako ga shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na Sin Tu Mingde ya yi cewar, gasar wasannin Olympic ta Beijing ba ma kawai wata gasar wasanni ba, haka kuma ma'anarta tana da zurfi sosai."(Bako)