Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-15 09:02:23    
An fara yin bikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Songyuan

cri

Ran 15 ga wata, an fara yin bikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Songyuan da ke lardin Jilin a arewa maso gabashin kasar Sin.

Da misalin karfe 7 da minti 15 da safe, an fara yin bikin yawo da wutar wasannin Olympic na Beijing a wurin shakatawa na Olympic da ke birnin Songyuan. Daga bisani kuma, wutar "gajimare mai kawo alheri " za ta isa wuri na karshe watau dandalin Dongzhen da ke birinin Songyuan. Masu dauke da wuta su 110 za su shiga cikin bikin mika wuta a birnin Songyuan, kuma tsawon hanyar da za a bi wajen mika wutar zai kai kilomita 8.25.

A gun bikin fara yawo da wuta da wurin da za a cunna wuta, za a yi wake-wake da raye-rayen da ke da halayyen musamman na kabilar Man, kuma a kan hanyar da za a bi wajen mika wuta za a yi raye-raye na musamman na kabilar Mongolia, kuma a gun bikin mika wuta, za a yi wasannin kayan kidan da aka yi da tsirkiyoyi watau Ma Touqin, kuma zai kago wani sabon bajintar duniya.

Daga bisani kuma, za a bi hanyoyin mota har kilomita 265, a wannan ranar da yamma, wutar wasannin Olympic na Beijing za ta isa birnin Jilin da ke lardin Jilin.(Bako)