Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-14 19:53:19    
Bikin nishadi na"shafa maka bakin yumbu" na kabilar Wa ta kasar Sin

cri

A birnin Lincang na lardin Yunnan da ke kudancin bakin iyakar kasar Sin, da akwai wata karamar kabila ta musamman mai suna Wa. A farkon watan Mayu na kowace shekara, 'yan kabilar Wa da ke zama a nan sukan shirya bikin nishadi da ake kira "shafa maka bakin yumbu". To jama'a masu sauraro cikin shirinmu na yau, za mu kai ku ziyara garin kabilar Wa mai ban mamaki, don ganin yadda ake yin wannan biki.

"A wureren da ake yin bikin shafa maka bakin yumbu, ba a bambanta kabilu, dukkan mutane suna shafa wa junansu bakin Yumbu, idan an shafa wa tsofaffi bakin yumbu, ana nufin fatan lafiya da tsawon rai gare su, idan aka shafa wa 'yan mata bakin yumbu wato ana fatan za su samu soyayya mai dadi, idan an shafa wa yara bakin yumbu kuma ana fatan za su girma lami lafiya. Idan an shafa bakin yumbu a fuskar wani, wato zai yi farin ciki har shekara daya, idan an shafa wa wani bakin yumbu a duk jikinsa kuma, zai yi zaman alheri har duk tsawon rayuwarsa."

Mr. Wei Cheng, shugaban hukumar al'adu ta gundumar Cangyuan ta kabilar Wa mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke birnin Lincang na lardin Yunnan shi ne ya yi wannan magana. To, mene ne ma'anar bikin "shafa maka bakin yumbu"? Yanzu bari mu yi muku bayani a kan wannan biki.

Bikin shafa maka bakin yumbu ya zo ne daga wata kyakkyawar tatsuniya. An ce a zamanin da, 'yan adam ba su iya sakar zawwati ba, sukan sanye da fatun namun daji, wani sa'i ma har sun yi tsirara domin gudun farmakin da namun daji suka yi musu, kuma sukan shafa wa jikunansu bakin yumbu domin rigakafin cizon sauro da hasken rana. A kwana a tashi, irin wannan al'adar shafa wa jikunansu bakin yumbu ta zama wani bikin da akan yi domin kau da alkaba'i da abubuwa masu dafi.

Kabilar Wa wata kabila ce wadda take girmama launin baki, 'yan kabilar suna ganin cewa, launin baki ya fi kayatarwa. Sabo da haka a gun bikin "shafa maka bakin yumbu", wanda ya fi baki ya fi kyaun gani. Mr. Wei Cheng, shugaban hukumar al'adu ta gundumar Cangyuan ta kabilar Wa mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke birnin Lincang ya gaya wa wakilinmu cewa, "Da ma mu 'yan kabilar Wa mun mai da launin baki a matsayin launi mafi kayatarwa, bayan da ka halarci wannan biki, ka iya jin cewa fannin al'adun kabilar Wa yana da kyaun gaske, bayan da ka shafe kwana daya kana yin zaman mutane 'yan kabilar Wa, ka iya dandana hakikanan abubuwan da ke cikin al'adun kabilar".

Ko da yake an yi manyan sauye-sauye cikin shekara da shekaru da suka wuce, amma har ila yau 'yan kabilar Wa na gundumar Cangyuan ta kabilar Wa mai ikon tafiyar da harkokin kanta suna cin gadon wannan bikin gargajiya. Dalilin da ya sa suka yi haka shi ne, wannan ba wata hanyar da ake bi ba ce domin yin nishadi kawai, muhimmin abu shi ne bikin ya zama wata hanyar da ake bi don cin gado da ba da kariya ga al'adun gargajiya na kabilar. ya kasance da babban karfin al'adun da ba a yi amfani da shi ba a gundumar Cangyuan ta kabilar Wa mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke birnin Lincang na lardin Yunnan, tun 'yan shekarun nan da suka wuce, gundumar ta yi kokarin bunkasa sana'ar yawon shakatawa kuma ta kaddamar da bikin nishadi na "shafa maka bakin yumbu", tana fatan irin wannan al'adun gargajiya zai iya samun babban ci gaba cikin zaman al'umma na zamani. Mr. Xiao Hong, direktan ofishin sana'ar al'adu na gundumar ya bayyana cewa, "Bayan da aka gudanar da bikin shafa maka bakin yumbu, an sa kaimi ga bunkasa sana'ar al'adu."

Jama'a masu sauraro, bayan da muka karanta wannan bayani, kila kun fahinta kadan game da kabilar Wa. Amma sai bayan da kuka sa kafafuwanku kan wannan yanki, kuma kun halarci bikin "shafa maka bakin yumbu" da aka yi a tudun Awa kawai, za ku iya fadakar da kanku da gaske kan halin rishin tsoro da rishin nitsuwa da mutane 'yan kabilar Wa ke bayyana, kuma za ku iya gane cewa lalle suna da kirki da sahihanci.

---- Tun dogon lokacin da ya wuce, gwamnatin kasar Sin ta mai da muhimmanci wajen yin amfani da kuma bunkasa da cin gadon harshen kabilar Tibet na kasar.

Harshen kabilar Tibet ya samu amfani daga fannoni daban- daban ciki har da fannin siyasa da tattalin arziki da al'adu, a jihar Tibet ana iya ganin rubuce-rubucen kalmomin harshen kabilar Tibet ko'ina wato kamar a kan kofofin kantuna, da alluna masu nuna hanya, da katuna farashin kayayyakin da ake sayarwa. Manoma da makiyaya wadanda yawansu ya wuce kashi 80 bisa 100 suna kallon shirye-shiryen telebijin da ake watsawa cikin harshen kabilar Tibet, 'yan makaranta na kabilar Tibet su ma suna koyon harshen kabilarsu a ko'ina. Ban da wannan kuma ana nan ana kokarin daidaitawa da kuma buga littattafai da bayanai cikin harshen Tibet, ayyukan da ake yi wajen bincike da kuma bunkasa manhaja na harshen Tibet sai kara yawa suke a kowace shekara.

1 2