
Ran 14 ga wata, bisa "tsarin kallon gasa a filin wasannin Olympics" na wasannin Olympics na Beijing da na nakasassu na Beijing da aka bayar, an yi kira ga 'yan kallo da kada su dauki ko wane irin take da kasida yayin da suke shiga filin wasannin Olympics, ciki har da kayayyakin farfaganda da na nuni-nuni kan fannonin kasuwanci, da adinai, da siyasa, da soja, da yankin kasa, da hakkin 'dan Adam, da kiyaye zaman lafiya, da kiyaye dabobi.

Mr. Li Yong ma'aikacin sashen kula da harkokin mutane masu aikin sa kai na kwamitin shriya wasannin Olympics na Beijing ya ce, wannan tsari ya dace da tsarin Olympics. Idan 'dan kallo ya dauki take ko kasida yayin da yake shiga filin wasannin Olympics, mutane masu tsaro za su bincike kayayyakin da yake dauka, kuma za su daidaita irin wannan batu bisa tsarin kallon gasa a filin wasannin Olympics.
|