Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-14 17:26:27    
Kasar Sin tana kokarin aiwatar da tunanin "shirya wata gasar wasannin Olympic da ke kiyaye muhalli"

cri

"Shirya wata gasar wasannin Olympic da ke kiyaye muhalli" na daya daga cikin tunani uku da kasar Sin take bi wajen shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing. Sabo da haka, lokacin da kasar Sin take shirya wannan gasa, tana kokari sosai wajen aiwatar da wannan tunani, kuma ta samu dimbin kyawawan sakamako.

A cikin shekaru 7 da suka gabata bayan da birnin Beijing ya samu izinin shirya gasar wasannin Olympic a shekara ta 2008, kasar Sin ta samar da jerin dakuna da filayen motsa jiki masu inganci. Lokacin da ake gina wadannan dakuna da filayen motsa jiki, kasar Sin ta mai da hankali sosai wajen tsimin makamashi da ruwa, kuma ta yi amfani da kayayyakin da ba za su gurbata muhalli ba. Alal misali, birnin Beijing birni ne da ke karancin ruwa sosai. Sabo da haka, yaya za a iya yin tsimin ruwa da sake yin amfani da ruwan da aka taba yin amfani da shi a cikin dakuna da filayen motsa jiki ya zama batun da ke matsayi mafi muhimmanci lokacin da ake zanayya wadannan dakuna da filayen motsa jiki. Mr. Hu Jie wanda ya zanayya lambun shan iska ta Olympic, wato wani wurin da ke amfani da ruwa da yawa a cikin cibiyar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing ya bayyana cewa, "Birnin Beijing birni ne da ke karancin ruwa sosai. Wannan lambun shan iska ta gandun daji ta Oympic ta Beijing lambun shan iska ce mafi girma a nan kasar Sin wajen yin amfani da ruwan da aka riga aka yi amfani da shi kuma aka sake sarrafa shi. Wato ba a yi amfani da ruwan sha ba a cikin wannan lambun shan iska domin yin tsimin ruwa."

Yanzu ana amfani da irin wannan ruwan da aka sake sarrafa shi wajen tsabtace titi da yi wa bishiyoyi din ruwa. Bayan da birnin Beijing ya samu izinin shirya gasar wasannin Olympic ta karo na 29, an riga an gina tasoshin sake sarrafa ruwan da aka yi amfani da shi guda 10 a Beijing, yawan irin wannan ruwan da aka sarrafa ya kai kubik mita miliyan 480 a shekarar da ta gabata.

Bugu da kari kuma, ana amfani da makamashin karfin hasken rana da na karfin iska da zafin da ake samu daga karkashin kasa a cikin dakuna da filayen motsa jiki da aka gina domin gasar wasannin Olympic ta Beijing. Ya zuwa yanzu yawan makamashin da ba za su gurbata muhalli ba kuma ake amfani da shi a cikin dakuna da filayen motsa jiki na gasar Olympic ta Beijing zai kai fiye da kashi 26 cikin kashi dari. Sakamakon haka, yawan carbon dioxide da za a rage fitarwa zai kai kimanin ton 570 a kowace shekara.

A waje daya kuma, birnin Beijing ya kara karfin kyautata ingancin iskarsa. A lokacin da ake shirya gasar, birnin Beijing ya kaurace wasu ma'aikatu na kamfanin narka karfe da bakin karfe na Babban Birni. Mr. Mu Huaiming wanda ke kula da aikin kiyaye muhalli a wannan kamfani ya bayyana cewa, "Yawan abubuwa masu gurbata muhalli da kamfaninmu zai fitar a shekara ta 2008 zai ragu da kashi 50 cikin kashi dari ko fiye bisa na makamancin shekara ta 2007."

Domin gwamnatin kasar Sin tana ta yada tunanin kiyaye muhalli a kullun, yanzu wannan tunani ya riga ya shiga cikin zukatan jama'ar kasar Sin. Yarinya Ye Lu mai shekaru 17 da haihuwa yanzu ta soma yada tunanin kiyaye muhalli tun daga lokacin da take da shekaru 10 da haihuwa. Ana kiranta "yarinya ce da ke kiyaye muhalli". Ta taba dasa itatuwa a cikin hamadan da ke jihar Mongoliya ta gida, kuma ta taba karbar batir da aka yi amfani da su, kuma ta yada ilmin kiyaye muhalli a kan shafin internet. Ye Lu ta ce, "Ya kamata a yada tunanin kiyaye muhalli ga kowane mutum. Idan kowa yana da irin wannan tunani, shi ke nan, batutuwan batir da shara da tsimin ruwa ba za su zama batutuwa da ake damuwa ba. Yanzu ba mu dauki wasu makatan kiyaye muhalli kawai ba, mun fi mai da hankali kan yadda tunanin kiyaye muhalli."

Kokarin da yarinya Ye Lu ta yi ya samu amincewa daga jama'a. Ta zama mai rike da wutar wasannin Olympic har sau biyu a gun gasar wasannin Olympic ta Athen da ta Beijing.