Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-14 15:13:02    
Bikin nishadi na"shafa maka bakin yumbu" na kabilar Wa ta kasar Sin

cri

Harshen kabilar Tibet yana da tarihin da ya shafe shekaru fiye da 1,300, wato yana daya daga cikin nau'o'in babbaku mafi dogon tarihi na duniya.

---- Kwanan baya, an mika wutar wasannin Olimpic a gundumar Leishan da birnin Kaili cikin yankin kabilar Miao da ta Tong mai ikon tafiyar da harkokin kansa da ke kudu maso gabashin lardin Guizhou. A nan da akwai tsofaffin kauyuka masu yawa na kabilar Miao, kuma muryar wakokin kabilar ta game ko'ina. A nan da akwai bukukuwan kabilu da yawansu ya kai 400, ana yin kwado da linzami mafi kyaun gani a nan, kuma ya kasance da muhallin halittu mai kyau, sabo da haka wurin ya yi suna kamar "wuri mafi kyaun gani na duniya".

Wata sigar musamman da aka bayyana a gun bikin mika wutar wasannin Olimpic a kudu maso gabashin lardin Guizhou ita ce, an ratsa wasu tsofaffin kauyuka masu kayatarwa na kabilar Miao da ta Tong don bai wa juna wutar. Kauyen kabilar Miao da aka fara mikar wutar yana da tarihi fiye da shekaru 100, dakunan da aka gina suna dogaro bisa tsaunuka, kuma ruwan kogi mai tsabta yana malalawa bisa gindin tsaunukan.

Akan ce haka, yankin da ke kudu maso gabashin lardin Guizhou "teku ne na wake-wake da raye-raye", a nan duk wanda ke iya magana ya iya waka, kuma duk wanda ke iya tafiya da kafafuwansa ya iya rawa.

A nan kuma duk wanda ke iya dinkin tufafi ya iya yin kwado da linzami, sabo da haka tufafin 'yan kabilar Miao suna da kyaun gani kwarai da gaske. Ban da wannan kuma yankin da ke kudu maso gabashin lardin Guizhou "gari ne mai bukukuwa da yawa", yawan bukukuwan kabilu da na gargajiya da ake yi a kowace shekara a duk yankin ya kai kusan 400. Akan yi wasanni iri-iri a gun wadannan bukukuwa kamar su, yin wake-wake da raye-raye, da karon shanu da sukuwar dawaki, da wasan tseren kwalle-kwallen dodo da kunna fitilun dodo.

Sabo da ya kasance da kyakkyawan muhallin halittu da hakikanan abubuwan al'adun kabilu na tarihi a yankin da ke kudu maso gabashin lardin Guizhou, shi ya sa hukumar UNESCO ta MDD ta tsai da cewa, yankin nan ya zama daya daga cikin manyan wurare 10 masu ban sha'awa wajen yawon shakatawa na duniya, kuma asusun al'adun gargajiya na duniya ya tsai da cewa, wannan yanki ya zama daya daga cikin wurare 18 na duniya wajen kiyaye al'adun gargajiya na kabilu

A yankin da ke kudu maso gabashin lardin Guizhou, fadin shingen bishiyoyi ya kai kashi 62 bisa 100, fadin kungurmin daji na wannan yanki kuma ya kai kadada dubu 160, jimlar mutane na duk yankin kuma ta wuce miliyan 4 da dubu 410, yankin nan kuma yana da kabilu 33 ciki har da kabilar Miao da ta Tong da ta Han, yawan 'yan kananan kabilu ya kai kusan kashi 83 bisa dukkan mutanen yankin.


1 2