Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-14 11:08:19    
An kawo karshen mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Changchun

cri

Yau 14 ga wata da safe, an kammala bikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Changchun da ke lardin Jilin a arewa maso gabashin kasar Sin cikin nasara.

An fara yin bikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a cibiyar motsa jiki ta birnin Changchun, mai dauke da wuta na farko shi ne Mr. Wang Jiaqi watau mutum mai nazari a cibiyar nazarin ilmin injiniya ta kasar Sin. A karshe dai, wutar wasannin Olympic na Beijing ta isa dandalin idon ruwa na wurin shakatawa na Sculpture na birnin Chuangchun. Tsawon hanyar da aka bi wajen mika wutar wasannin Olympic na Beijing ya kai kilomita 9, masu dauke da wuta su 218 sun halarci wannan biki, mai dauke da wuta na karshe ita ce matar da ta sami lambobin yabo na azurfa wajen gudu kan kankara na Skating a gun gasar wasannin Olympic da aka yi a lokacin sanyi a Nagano na kasar Japan da Salt Lake city na kasar Amurka.

A wannan rana da yamma, ayarin motocin gasar wasannin Olympic na Beijing zai bi hanyar mota, don zuwa birnin da za a yi bikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing watau birnin Songyuan da ke lardin Jilin a kasar Sin(Bako)