Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-11 20:25:39    
Waiwaye adon tafiya(10)

cri

Inda yau za mu ci gaba da gabatar muku shirinmu na "waiwaye adon tafiya", wanda kuma zai kasance na karshe a cikin jerin shirye-shiryenmu na musamman na murnar cikon shekaru 45 da sashen Hausa na rediyon kasar Sin ya fara aiki, kuma ni ce Lubabatu ke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.

Masu sauraro, a watan Agusta na shekarar da muke ciki, sashen Hausa zai dauki wasu sabbin ma'aikata, wato wasu daliban da suka gama karanta harshen Hausa a jami'a, to, ga shi yau na gayyaci wasunsu zuwa filinmu na "waiwaye adon tafiya", wato su Lami da Murtala da kuma Bako, don mu yi hira da su. To, barkanku da zuwa filinmu na "waiwaye adon tafiya", kuma da farko dai, ko za ku gabatar da kanku zuwa ga masu sauraronmu?

Lami:To, sannunku, masu sauraro, sunana Lami, zan gama karatu a jami'ar koyon ilmin watsa labaru ta kasar Sin dake nan birnin Beijing, na fito daga birnin Tianjin wanda ke kusa da Beijing. A shekaru 4 da suka wuce, na shiga jami'a don koyon harshen Hausa, yanzu, ina gwajin aiki a gidan rediyon kasar Sin, ina farin ciki sosai don samun aikin da nake so.

Murtala:To, aminai masu sauraronmu, assalamu alaikum! Sunana Murtala, daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin nike muku gaisuwa da fatan alheri. Na zo daga birnin Nanjing da ke kudu maso gabashin kasar Sin. Na gama karatun Hausa a sashen Hausa na jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing a wannan shekara.

Bako: To, masu saurarommu, assalamu alaikum, yau dai ina murna da farin ciki sosai sabo da samun damar mu'ammala tare da ku daga nan sashen hausa na rediyon kasar Sin a cikin filin musamman da Lubabatu ta ja akalarsa, ni bako ne, kuma a shekaru hudu da suka gabata, na zama wani dalibi mai koyon harshen Hausa, a ganina, Allah shi ne ya albarkace ni in koyi wannan harshe.

Lubabatu:To, mun gode. Hausawa su kan yi mamaki idan sun ji Sinawa na yin magana da Hausa, amma a hakika dai, yanzu akwai jami'o'i biyu a nan kasar Sin da ke da sashen koyon harshen Hausa, kamar Lami, ta zo ne daga jami'ar koyon ilmin watsa labarai da ke nan birnin Beijing, kuma akwai sashen koyon harshen Hausa a can jami'ar. Bayan haka, ga Bako da Murtala, sun zo ne daga jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing. To, yanzu ko za ku dan bayyana mana yadda sashen Hausa yake a jami'arku da kuma karatunku a wurin?

Lami: Sashen Hausa daya ne daga cikin sassan kwalejin koyon harsunan kasashen waje na jami'armu, wato jami'ar koyon ilmin watsa labaru ta kasar Sin. Akwai dalibai goma a cikin ajinmu, maza hudu, kuma mata shida. Muna da malamai uku, wato malam Usman da malam Lawal da kuma malam Baralabe.

Bako: Ni da Murtala mun zo ne daga jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing. Kamar sanin kowa ne, jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing wata sananniyyar jami'a ce wajen koyon harshe, haka kuma harshen hausa wani muhimmin harshe ne a cikin jami'armu, a matsayinsa na daya daga cikin manyan harsunan uku a Afrika, fannin nazarin Hausa ya sami karbuwa a tsakanin dalibammu.

Murtala: An kafa sashen Hausa a jami'armu ne a shekarar 1964, yanzu haka a ajinmu, akwai dalibai 24 masu koyon harshen Hausa, ciki har da maza 16 da mata 8. Muna da malamai biyu, wato malama Suwaiba da malam Shekarau, wadanda suka taba koyon Hausa a jami'ar ABU, Zaria.

Lubabatu:To, mun gode da bayanin da kuka yi. To, yau a wannan filinmu na "waiwaye adon tafiya", na bayyana ku matsayin sabbin ma'aikatan da sashen Hausa zai dauka, amma a ganina, masu sauraronmu sun riga sun saba da sunayensu, sabo da na san kun fara gwajin aiki a nan sashen Hausa tun daga watan Agusta na shekarar bara, kowace rana kuna zuwa kuna fassara labarai kuna yin wasu shirye-shirye, musamman ma wakoki da kide-kide, sabo da haka, ina tsammanin tun tuni masu sauraronmu sun saba da sunayenku. To, tambayata ita ce shin yaya sashen Hausa ya burge ku a tsawon lokacin da kuke aiki a wajen, kuma ko kun karu kun sami wani abu daga aikin da kuka yi?

Murtala:Lalle, abin da ya fi burge ni a nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin shi ne, akwai kyakkyawan yanayin karatu a nan. Wato kamar yadda malam Bahaushe ya kan ce, matambayi ba ya bata. A ranar farko da na zo nan sashen Hausa na CRI, na ga dukan ma'aikatan sashen Hausa suna nan suna aiki tukuru ba ji ba gani, amma ba su daina koyon harshen Hausa ba, alal misali, idan wani ya gamu da wata matsala a kan harshen Hausa, ya kan tattauna tare da sauran ma'aikata. Lalle wannan al'amari ya ba ni kwarin gwiwa sosai da sosai wajen ci gaba da koyon Hausa ba tare da tsayawa ba bayan da na gama karatu a jami'a.

Lami:A ganina, abin da ya fi burge ni shi ne, kyakkyawar huldar dake tsakanin ma'aikatan gidan rediyon kasar Sin. A cikin wannan hali, kowa na iya aiki da kyau.

Lubabatu:Bako, kai fa, ko akwai abin da ya karu da shi?

Bako:A shekara daya da ta gabata, lokacin da nake aikin dare wata rana, wani dan kasar Camerron ya buga mana waya, ga shi kuma, a albarkacin wancan lokaci na kusantowar karamar salla, yayin da na tambaye shi, ko da wani abun ne, sai abin da ya amsa ya fi burge ni, ya ce, " to, malam Bako, ba kome, sai don gaishe ka kawai da karamar salla, da kuma mun gode. Daga nan ne, sai na sani aikinmu ya yi muhimmanci sosai.

Murtala: To, a ganina, dukanmu mu uku, muna ganin cewa, bayan gwajinmu a nan sashen Hausa na CRI, Hausarmu ta sami kyautatuwa kwarai da gaske, kuma ba ma kawai mun karo ilmi a fannin harshen Hausa ba, hatta ma mun san yadda za mu yi don zama wani kyakkyawan dan jarida, a ganina, wannan yana da muhimmanci kwarai da gaske.

Lubabatu:To, gaskiya kun yi kokari, kuma na yi farin ciki sosai da jin abubuwan da kuka karu da su a fannoni daban daban a cikin shekara kusan daya da kuke gwajin aiki a nan sashen Hausa. To, kun san a ran daya ga watan Yuni na wannan shekara, sashen Hausa ya cika shekaru 45 da aiki, a cikin shekarun nan 45, bisa kokarin da sashen Hausa wadanda suka gabata har zuwa yanzu suka yi, sashen Hausa ya ci gaba sosai, kuma ga shi yau tsoffin ma'aikatan sashen Hausa da suka kafa sashen sun riga sun yi ritaya, kuma ku za ku kasance tamkar "sabon jini" ga sashen Hausa, za ku ci gaba da daukar nauyinsu, to, ko me za ku fada a daidai wannan lokaci?

Lami: Ina fatan tsoffin ma'aikatan sashen Hausa wato malamanmu za su jin dadin zaman rayuwarsu bayan da suka yi ritaya, kuma zan yi iyakacin kokari wajen aiki ba tare da kasala ba. Zan gaji aikinsu da kuma ladabin sashen Hausa don daukaka cigaban shirye-shiryenmu.

Murtala:To, da farko dai, bari in taya sashen Hausa na CRI murnar cika shekaru 45 da kafuwa. A daidai wannan lokaci, ina alfaharin samun zarafin zama wani ma'aikaci a nan. shi ya sa bari in ci gaba da kyautata harshen Hausana, da kokarta ba tare da kasala ba wajen bayarwa masu sauraronmu shirye-shirye masu ban Sha'awa.

Lami: Sashen Hausa:barka da ranar haihuwa!

Murtala:Barka da ranar haihuwa, sashen Hausa!

Bako:Sashen Hausa, barka da ranar haihuwa!

Lubabatu: Masu saurare, yau ga shi shekaru 45 sun wuce, har jariri ya girma ya zama dattijo. Kamar yadda Hausawa kan ce, "waiwaye adon tafiya", yau muna taya murnar cikon shekaru 45 da kafuwar sashen Hausa ne, ba ma kawai domin murnar nasarorin da muka cimma ba, amma domin murnar wannan sabon mafari a tarihin sashen Hausa, sabo da daga nan ne, sashen Hausa na rediyon kasar Sin zai fara sabuwar tafiya tare da samun sabon ci gaba. To, masu sauraro, duka duka wannan shi ya kawo karshen jerin shirye-shiryenmu na "waiwaye adon tafiya", tare da fatan kun ji dadinsu, da haka ni Lubabatu daga nan Beijing ke cewa, a kasance lafiya. (Lubabatu)