Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-11 20:24:13    
Ina da aniyar zama wani mutum kakkarfa har abada

cri

Aminai 'yan Afrika, a yau dai, zan dan gutsura muku wani bayani kan wani mazaunin birnin Nanjing na lardin Jiangsu na kasar Sin wanda ya yi alfaharin zama mai dauke da fitilar wasannin Olympics na Beijing. Sunansa Bei Wanli, wanda shi ne nakasasshe saboda ya kasance mai hannu daya sakamakon wani hadari da ya wakana lokacin da yake aiki. Ko da yake Mr. Bei yana da hannu daya kawai, amma ya nuna karfin zuciya har ya shiga gasar tseren mutum daya cikin wasanni uku wato wasan Triathlon dake kunshe da wasan iyo, da gudun fanfalake da kuma wasan tseren keke kan hanyar mota har fiye da sau 20, da aka taba gudanar a ciki da wajen kasar. Saboda haka ne, ake kiransa " Mutum kakkarfa mai hannu daya".

A cikin mutane masu sha'awar wasan tseren mutum daya kakkarfa cikin wasanni uku na kasar Sin, ba wanda bai san sunan Mr. Bei Wanli ba. Shi wani siriri ne mai shekaru 57 a duniya. Yau da shekaru fiye da 30 da suka gabata, ya rasa hannu guda a wani hadari. Abokansa sun ce lallai abun al'ajabi ne gare shi saboda ya nuna bajinta wajen shiga irin wannan wasa duk da cewa yana da nakasa. Amma Mr. Bei Wanli ya fadi abun ake cikin zuciyarsa cewa: " Na gane sosai cewa, wajibi ne na yi kokarin samun nasara kan kaina in na shiga irin wannan wasa mai wahala. Ko da yake wasan nan, wasa ne na wuce iyaka, amma ina da aniyar cimma burina na more irin wannan wasa".

Aminai masu saurare, ko kuna sane da cewa, irin wannan wasa ya samo asali ne daga jihar Hawaii ta kasar Amurka a shekarar 1974; An kuma mayar da shi a matsayin wasannin Olympics a hukumance a shekarar 2000. Wasan ya tanadi cewa, duk kowane dan wasa dole ne ya kammala wasan iyo na tsawon kilo-mita 1.5, da wasan tseren keke kan hanyar mota na tsawon kilo-mita 40 da kuma wasan gudu na dogon zango na kilo-mita 10 dake karkarar birni a cikin sa'o'I uku da minti hamsin. A yanzu haka dai, malam Bei Wanli ya zama wani nakasasshe daya tilo a kasar Sin wanda ka iya halartar irin wannan wasa na wuce iyaka. Kuma ya shiga cikin irin wannan gasa ne a shekarar 1999 a birnin Qingdao na lardin Shandong na kasar Sin, inda ya fi janyo hankaln masu kallo saboda shekarunsa ya rigaya ya kai 47 da haihuwa.

Lallai Malam Bei Wanli ya yi farin ciki matuka da samun babban goyon baya daga bangarori daban-daban na zamantakewar al'ummar kasar. Sa'annan ya lashi takobin bada kwarin gwiwa ga sauran nakasassu masu tarin yawa bisa kokarin da yake yi. Yana mai cewa: 'Babban burina shi ne mu nakasassu mu iya samun kyakkyawar rayuwa daidai kamar yadda sauran mutanen da ba su da nakasa muddin na bada misali a matsayin gwaji a cikin wasan tseren mutum daya kakkarfa cikin wasanni uku'.

Daidai bisa wannan makasudi ne, Malam Bei Wanli yake nacewa ga samun horo da shiga gasanni. Amma, mutane masu yawan gaske suna shan wahala wajen shiga irin wannan wasa na tseren mutum daya cikin wasanni uku, balle wani nakasasshe mai hannu daya. Musamman ma tseren keke kan hanyar mota ya zamo karan tsaye gare shi wajen shiga gasanni. Wata rana, ya ji rauni a fuskarsa har hakora 3 sun fadi daga bakinsa lokacin da yake yin horo.

A yanzu haka dai, Malam Bei Wanli ya kama mukamin babban sakataren hadaddiyar kungiyar wasan tseren mutum daya kakkarfa cikin wasanni uku ta birnin Nanjing, inda akwai mutane sama da dubu daya da suke sha'awar irin wannan wasa. Ya fada wa wakilinmu cewa: " Na tuna fa, muddin mu fararen hula dukkanmu sun kasance mutane karfafa, to Liu Xiang nawa ne za a iya samo a kasarmu"?

Yayin da Malam Bei yake tabo magana kan samun damar zagayawa da fitilar wasannin Olympics na Beijing, ya yi murmushi da fadin cewa: " Lallai na yi alfamar zama mai dauke da fitilar wasannin Olympics. Na samu wannan dama ne ba domin komai ba sai kawai domin fahimtar da aka samu a game da wasan tseren mutum daya kakkarfa cikin wasanni uku. Ina so in zama wani mutum kakkarfa har abada. Kuma cike nake da kyakkyawan fatan wutar wasannin Olympics za ta karfafa mini zafin nama da kuma more buri da kuma ganin mutane mafiya yawa su shiga irin wannan wasa". ( Sani Wang)