
Yau 11 ga wata, an shiga rana ta farko wajen yin bikin mika wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a lardin Hei Longjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin.

Birnin da za a yi bikin mika wutar wasannin Olympic na farko a Lardin Hei Longjiang shi ne hedkwatar lardin watau Harbin. Da misalin karfe 8 da safe, an yi bikin mika wutar wasannin Olympic a dandalin hasumiya da aka gina domin tunawa da yaki da bala'in ambaliyar ruwa da ke birnin Harbin, masu dauke da wuta na farko su ne Zhang Dan da Zhang Hao watau zakarun gasar wasannin gudu a kan kankara ta Skating da aka yi da mutane biyu-biyu.

Daga bisani kuma, wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta bi wurin shakatawa ta Stalin da hanyar zumunta da babbar gada da aka gina a kan tekun Song Huajiang da tsibirin Tai Yangdao da sauran shahararrun wurare, a karshe dai za a isa wuri na karshe watau dandalin Tai Yangshi da ke tsibirin Tai Yangdao. Tsawon hanyar da za a bi wajen mika wuta zai kai kilomita kimanin 14.86, masu dauke da wuta su 208 za su shiga cikin wannan biki.(Bako)
|