Ya kamata dakin sayar da abinci ya biya kudin diyya ga masayen abinci.wata kotu ta yanke hukunci cewa kamata ya yi dakin sayar da abinci ya biya kudin diyya ga wani tsoho wanda ya cin abinci a dakin ya yi fama da ciwon zuciya sabo da fadan da aka yi tsakanin masayen abinci da sabis. Tsohon nan da ake kiransa Xiao yana da shekaru 70 da haihuwa,wata rana da yake cin abinci a dakin sayar da abinci a yankin Liwana na birnin Guangzhou,wata fada dake tsakanin masaye abinci biyu da sabis ta barke,sai tsohon ya tsorata ya kuma ji ciwon zuciya. Da ganin hakan sauran maciya abinci sun firgita sun fita daga dakin,aka kai tsohon asibiti ta motar ba da agajin gaggawa. Kudin asibitin da aka kashe domin ceton wannan tsohon ya kai kudin Sin RMB Yuan dubu shida dai shida da ashirin da shida.Kotun ta yanke hukunci cewa kamata ya yi dakin sayar da abinci ya biya rabin kudin asibitin da aka kashe domin tsohon dalili kuwa shi ne ya kasa kiyaye zaman odar dake cikin dakin cin abinci.
An daura motar mai cin bashi da sarka domin tilasta masa da ya biya bashi. Wata hanya ce da ta fi dacewa da aka tilasta mai ci bashi ya biya bashi.Ma'aikata na hukumar kula da filaye da gidaje ta lardin Hainan sun yi amfani da wata dabara domin tilasta mai cin bashi ya biya bashi. A ranar talata da ta shige,sun daura motar mai cin bashi Lin Libao da sarka wanda ya yi ariyar biyan bashi da wasu watanni,inda suka bukace shi da ya biya bashi,in ba ya biya ba ba a saki motarsa ba. Duk da haka Lin Libao ya kirawo 'yan sanda,daga nan 'yan sanda sun fara binciken batu.
Wata diya ta fi so kula da iyayenta na rana. Wata diya mai suna Jin Lian wadda take da shekaru 16 da haihuwa tana daukar hankulan mutanen gundumar Anding na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin sabo da ta kin tayin da iyayenta na haihuwa suka yi mata na yin zaman jin dadi tare da su,maimakon haka ta ce ta fi son kula da iyayenta na rana. Jin Lian,yarinya ce a babbar makarantar sakandare.yayin da take da shekara daya da haihuwa,tsoho Mo Keli mai yawan shekaru 79 da haihuwa da matarsa Wang Yubo mai yawan shekaru 70 a yanzu sun dauke ta a matsayin diya. A halin yanzu tsoho Mo Keli yana fama da ciwon inna,matarsa tana da fama da ciwon yanar ido. Jin Lian ta shirya musu abinci bayan makaranta. Ko wace rana da sassafe, Jin Lian ta tashi ta shirya abincin karya kumallo,ta sanya abincin da ta dafa a gefen gadonsu ta tafi makaranta ta kuma shirya musu abinci na rana da na yamma. Kwanan baya Jin Lian ta gano iyayenta na haihuwa wadanda suke da masana'anta a yanzu,sun bukace ta da ta koma gida.amma Jin Lian ta kin tayin da suka yi, ta ce ba ta yi zama fiye da rabin shekara da iyayenta na haihuwa ba domin iyayent na rana suna bukatarta da ta kula da su.
Wani kuku ya yi kuskure wajen dafa abinci. Wani kuku mai suna Yan ya yi babban kuskure yayin da ya shirya abinci.ya kuskura ya sa man da ake amfani da su a cikin masana'anta a matsayin man girki, shi ya sa mutane sama da 32 sun sha guba,aka kai su asibiti cikin gaggawa aka ba su magani. Wannan al'amari ya faru ne a birnin Zhengzhou,babban birnin lardin Henan da ke tsakiyar kasar Sin. Yawancin masu sha guba 'yan ci rani ne da suke ginawa gidaje na kusa. Da aka gama cin abincin rana, da wajejen karfe biyu wasu fara jin ciwo mai zafi,sai aka kai su asibitin aka yi musu bincike,daga baya aka gane cewa sun ci abinci ne mai guba.
|