Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-10 17:47:20    
Kungiyar 'yan wasa ta kasar Malaysia na share fage kan wasannin Olympics na Beijing

cri

Za a bude wasannin Olympics na Beijing na shekarar 2008 a watan Agusta na shekarar da muke ciki, kungiyar 'yan wasa ta kasar Malaysia ita ma za ta shiga wannan gasa. A karshen watan Yuni na shekarar 2007, kasar Malaysia ta nada tsohon shugaban kungiyar wasan hoki a fili ta kasar Mr. Ho Koh Chye da ya zama shugaban kungiyar wakilan 'yan wasa masu shiga wasannin Olympics na Beijing ta kasar Malaysia. Don fahimtar halin da kungiyar 'yan wasa ta Malaysia ke ciki wajen shiga wasannin Olympics na Beijing, wakilinmu ya kai ziyarar musamman ga Mr. Ho Koh Chye. Yanzu, ga cikakken bayanin.

A shekarar 1956, a karo na farko ne kasar Malaysia ta shiga wasannin Olympics, tun daga lokacin har zuwa yanzu, ban da wasannin wasannin Olympics na Moscow na shekarar 1980, kasar Malaysia ta halarci kusan dukkan wasannin Olympics. Amma, har zuwa yanzu, 'yan wasa na kasar Malaysia ba su samu ko wata lambar zinariya ta wasannin Olympics ba, saboda haka, kungiyar wakilan 'yan wasa ta Malaysia na fatan samun lambar zinariya ta farko a gun wasannin Olympics na Beijing, Mr. Ho Koh Chye ya gabatar da cewa,

"A wasannin Olympics na Barcelona da aka shirya a shekarar 1992, mun samu lambar tagulla ta gasar kwallon badminton, a wasannin Olympics na Atlanta na shekarar 1996 kuma, mun samu lambar azurfa daya, da lambar tagulla daya a gasar badminton. Muna fatan za mu samu wata lambar zinariya ta wasannin Olympics a gasar badminton ga kasar Malaysia a shekarar da muke ciki."

Mr. Ho Koh Chye ya yi harsashe cewa, akwai 'yan wasa na kasar Malaysia da yawansu ya kai kusan 30 za su shiga wasannin Olympics na Beijing, wadannan 'yan wasa za su shiga wasannin badminton, da daka tsalle cikin ruwa, da iyo, da tsalle-tsalle da guje-guje, da harba kibiya, da karate, da harbe-harbe, da tseren kwale-kwale, da tseren basukur, da dai sauransu.

Domin samun sakamako mai kyau a wasannin Olympics na Beijing, ba kawai kasar Malaysia ta gayyaci masu horar da 'yan wasanni daga kasashen ketare ba, a waje daya kuma ta aika da masu aiki da abin ya shafa da su yi bincike a birnin Beijing, don fahimtar muhallin gasa. Mr. Ho Koh Chye ya bayyana cewa,

"Mu kan horar da 'yan wasanni a kasashen ketare, ciki har da kasar Sin. Kamar misali, saboda mai horar da 'yan wasannin daka tsalle cikin ruwa na kungiyarmu ya fito ne daga kasar Sin, don haka, muna horar da 'yan wasannin daka tsalle cikin ruwa a birnin Kunming na kasar Sin a dukkan shekara. Kazalika, mu kan horar da 'yan wasanninmu a kasashen Korea ta kudu, da Australia, da kuma Amurka. A 'yan shekarun da suka wuce, masu horar da 'yan wasanni su kan aika da 'yan wasanni zuwa birnin Beijing, don samun horo, ko shiga gasa. A sakamakon haka, ya zuwa lokacin wasannin Olympics da za a shirya a watan Agusta na bana, 'yan wasanninmu za su san Beijing sosai, lallai ba za su ji kamar su yi gasa a wani sabon wuri ba."

Mr. Ho Koh Chye ya taba wakiltar kungiyar 'yan wasan hoki a fili don halartar wasannin Olympics na Tokyo na shekarar 1964, da na Mexico na shekarar 1968, bayan haka kuma, sai ya yi ritaya daga kujerar 'dan wasa, kuma ya soma aikin mai horar da 'yan wasanni. A shekarar 1992, Mr. Ho Koh Chye ya shugabancin kungiyar 'yan wasan hoki a fili ta kasar Malaysia, don halartar wasannin Olympics na Barcelona. A shekarar 2003, ya shugabancin kungiyar waki'an 'yan wasanni ta kasar Malaysiya bisa matsayinsa na shugaban kungiyar, don halartar wasanni na kudu maso gabashin Asiya da aka shirya a kasar Vietnam. Yanzu, a karo na biyu ne da zai shugabancin kungiyar wakilan 'yan wasanni ta kasar Malaysia, don shiga wasannin Olympics na Beijing. Saboda sau da yawa Mr. Ho Koh Chye ya halarci gagaruman wannani na duniya, don haka yana fahimtar hasashen wasannin Olympics sosai, yana adawa da ayyukan kaurace wa wasannin Olympics, don cimma burinsu na siyasa da wasu mutane na kasashen duniya suka yi. Ya ce,

"'Yan wasanni daga kasashe da shiyyoyi sama da 200 na dukkan duniya suna iya shiga wasannin Olympics, amma an kafa lambobin yabo guda uku kawai, wato lambar zinariya, da lambar azurfa, da kuma lambar tagulla, wannan na nuna cewa, ba kowane 'yan wasanni masu shiga gasa suna iya samun lambar yabo ba. Amma, wasannin Olympics na fa'idarsa, ko wani 'dan wasan suna iya yin cudanya da 'yan wasa daga sauran kasashe ta hanyar shiga wasannin Olympics, haka kuma suna iya sada zumunta a tsakaninsu. Hasashen wasannin Olympics shi ne, a bar dukkan 'yan wasa su shiga wasannin Olympics ba tare da la'akari da bambancin kabila, da harshe ko launin fata ba, kuma ba tare da sanya siyasa ba. Aikin dawa da wasannin Olympics na hana bunkasuwar wasannin motsa jiki, a gun wasannin Olympics da a kan shirya a kowane shekaru 4, mutane suna iya ganin wane ne ya fi kwarewa wajen motsa jiki a yanzu, amma idan a nuna adawa da wasannin Olympics, to 'yan wasan da suka yi kokari don shiga wasannin cikin dogon lokaci, za su rasa damar cimma burinsu. Bayan haka kuma, aikin adawa da wasannin Olympics zai hana sada zumunta a tsakanin 'yan wasa daga kasashen ketare, a waje daya kuma ya hana yaduwar hasashen wasannin Olympics. Saboda haka, na yi kira da cewa, kada a yi amfani da aikin motsa jiki don ya zama abin aiki na wasu mutane wajen cimma burinsu, ya kamata wadancan 'yan siyasa su yi nesa da wasannin Olympics."

A watan Agusta na shekarar da ta wuce, Mr. Ho Koh Chye ya zo nan birnin Beijing, don kawo ziyarar musamman ga halin da ake ciki kan gine-ginen filaye da dakunan motsa jiki na wasannin Olympics. Yana ganin cewa, birnin Beijing ya shirya sosai kan ayyukan share fage, kuma yana fatan za a samu nasarar wasannin Olympics na Beijing. Mr. Ho Koh Chye ya ce,

"Na yi imani cewa, birnin Beijing zai samu nasara wajen shirya wasannin Olympics, na fadi haka ne bisa fasahohin da na samu. Na halarci wasannin Olympics har sau uku, bayan haka kuma, na taba yin ziyara kan ayyukan share fage na wasannin Olympics na Beijing a shekarar da ta wuce, inda ba kawai na kai ziyara ga filayen motsa jiki, har ma na kai ziyara ga kauyen wasannin Olympics da aka gina domin 'yan wasa na kasashe daban daban na duniya, lallai na yi mamaki sosai kan ingantatun ayyukan share fage da Beijing ke yi. Bugu da kari kuma, na yi imani cewa, masu dauki nauyin wasannin Olympics na Beijing za su ba da tabbaci wajen shirya dukkan wasanni bisa hasashen wasannin Olympics, kuma za a yi wasannin na zaman daidai wa daida, kuma cikin adalci,. Ina fatan za a samu babbar nasara kan wasannin Olympics na Beijing!"