Tun daga ran 7 zuwa 9 ga watan nan da muke ciki, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya halarci taron shawarwarin da aka gudanar a Hokkaido na kasar Japan, a tsakanin shugabannin kasashe 8 masu arzikin masana'antu, wato G8 da na kasashe masu tasowa. A kan hanyar komawa gida, ministan harkokin waje na kasar Sin, Mr.Yang Jiechi, wanda ya yi wa shugaba Hu Jintao rakiya, ya bayyana cewa, a cikin kwanaki biyu da suka wuce, shugaba Hu Jintao ya halarci tarurruka da shawarwari sama da 20 a tsakanin bangarori da dama ko biyu biyu, tare kuma da cimma muhimman nasarori.
Mr.Yang Jiechi ya ce, a cikin 'yan shekarun baya, bisa taron shawarwarin da ke tsakanin G8 da kasashe masu tasowa ne, muhimman kasashe masu tasowa da kasashe masu sukuni sun yi musanyar ra'ayoyi tare kuma da daidaita matsayinsu, wanda kuma ya taimaka wajen bunkasa hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa da kuma masu ci gaba, da kuma daidaita matsalolin duniya. A gun taron na bana, an fi mai da hankali a kan tattalin arzikin duniya da sauye-sauyen yanayi da matsalar abinci da kuma makamashi, wadanda suke kasancewa matsalolin gaggawa da ke gaban gamayyar kasa da kasa. A game da matsalolin, shugaba Hu Jintao ya bayyana ra'ayoyin kasar Sin da manufofinta daga fannoni daban daban, tare kuma gabatar da jerin muhimman shawarwari.
Mr.Yang Jiechi ya bayyana cewa, a game da tattalin arzikin duniya, shugaba Hu Jintao ya gabatar da shawarar raya tsarin tattalin arzikin duniya da ke iya bunkasa cikin dorewa da tsarin kudin duniya mai jituwa da tsarin cinikin duniya mai adalci da kuma tsarin bunkasuwar kasashen duniya mai daidaici. Wannan fa karo ne na farko da Sin ta gabatar da manufarta a duniya dangane da raya tsarin tattalin arzikin duniya, wanda kuma ya nuna mana irin kokarin da take yi wajen samun moriyar juna daga bunkasuwar tattalin arzikin duniya bai daya.
A game da sauyin yanayi, Mr.Hu Jintao ya yi nuni da cewa, sauyin yanayi matsala ce da aka samu wajen neman ci gaba, kuma kamata ya yi a daidaita shi bisa tsarin samun dauwamammen ci gaba.
Sa'an nan, Mr.Hu Jintao ya yi nazari a kan dalilan da suka haddasa hauhawar farashin abinci a duniya, tare kuma da gabatar da matakan da ya kamata a dauka cikin gaggawa da kuma dogon lokaci wajen daidaita matsalar. Ya kuma yi kira ga kasashe daban daban da su dora muhimmanci a kan samar da binci, kuma su kyautata muhallin ciniki da inganta hadin gwiwa.
A game da makamashi, Mr.Hu Jintao ya jaddada cewa, Sin na tsayawa kan dogara bisa karfin kanta da bunkasa makamashi tare da yin tsiminsa a wajen samar da makamashi, kuma tana kokarin bunkasa makamashi iri daban daban da kuma bunkasa makamashin da ke iya sabuntawa, tana kuma dora muhimmanci a kan kyautata yin amfani da makamashi, har ma a bayane ne ya gabatar da burin da za a cimmawa wajen tsimin makamashi da rage fitar da iska mai guba. Ban da wannan, ya kuma gabatar da shawarar cewa, ya kamata kasashe daban daban su sa kaimi ga hadin gwiwarsu a fannin bunkasa makamashi, kuma su inganta hadin gwiwa a fannin bunkasa makamashin da ke iya sabuntawa da kyautata yin amfani da makamashi.
Daga karshe dai, Mr.Yang Jiechi, ministan harkokin waje na kasar Sin, ya ce, muhimman nasarorin da shugaba Hu Jintao ya cimma a wannan karo, za su amfana wa bunkasuwar kasar Sin da kuma hadin gwiwar da ke tsakaninta da sauran kasashe. Sauran wata daya kawai za a soma wasannin Olympics a birnin Beijing, kasashen duniya za su ci gaba da mayar da hankulansu a kan kasar Sin. Bunkasuwar kasar Sin cikin lumana za ta kara jawo wa kasar goyon baya da karbuwa daga duniya.(Lubabatu)
|