Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-10 14:07:05    
An fara mika wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Chifeng

cri

A ran 10 ga wata da safe da misalin karfe 8, an fara mika wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a birnin Chifeng na jihar Mongoliya ta gida mai ci gashin kanta.

An yi bikin fara mika wutar a lambun shan iska na nunin ala'du mai suna Cheboer, shugaban hukumar kula da yawon shakatawa na birnin Chifeng madam Na Risu ta dauki wutar yola ta farko da aka mika a birnin Chifeng. Daga baya, za a mika wutar a filin Yulong da lambun shan iska mai suna Haibeier da lambun shan iska mai suna Shibo da lambun shan isaka na nunin itattuwa mai suna Xingannanmi da sauran wurare masu ban sha'awa, wurin karshe da za a kai wutar a cikin shi ne filin jama'ar birnin Chifeng. Dukan tsawon hanyar ya kai kilomita 41.2, kuma tsawon hanyar da za a bi wajen mika wutar ya kai kilomita 6.2. Yawan jama'ar da za su dauki wutar yola ya kai 208.

A ran nan da yamma, za a kai wutar a birnin Haerbin, hedkwatar lardin Heilongjiang ta hanyar jirgin sama na musamman. Kuma za a shirya mika wutar a lardin Heilongjiang a ran 11 ga wata.(Abubakar)