
An cimma nasarar kammala aikin mika wutar wasannin Olympic na Beijing a biranen Erdos da Baotou a ran 9 ga wata da yamma.

Yau da karfe 8 da minti 15 na safe, an yi bikin fara mika wutar a birnin Erdos a gaban kabarin Genghis Khan. Masu mika wuta su 104 sun shiga cikin aikin mika wutar na tsawon hanya kilomita 6.3 a ran da safe.
Da misalin karfe 2 na yamma, an cigaba da mika wutar Olympic a birnin Baotou.
A ran 10 ga wata, za a mika wutar wasannin Olympic a birnin Chifeng na jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta.(Lami)
|