
Tun daga yau 9 ga wata, an fara mika wutar wasannin Olympics a birnin Erdos na jihar Mongoliya ta gida da ke arewacin kasar Sin.

A yau da safe, da misalin karfe 8 da minti 15, an gudanar da bikin fara mika wutar wasannin Olympics a gaban kabarin marigayi Genghis Khan, kuma dan wasan jefa faifan karfe kuma dan kabilar Mongoliya, wanda ya taba zama zakara a gun wasannin Olympics na nakasassu da aka gudanar a birnin Atlanta a shekarar 1996 ya fara mika wutar.
Za a bi ta wasu muhimman gine-gine lokacin da ake mika wutar wasannin Olympics a kabarin marigayi Genghis Khan, daga baya kuma, za a kai wutar zuwa filin Ghenghis Khan, wato inda za a kawo karshen mika wutar a birnin Erdos ke nan.

Gaba daya mutane 104 za su mika wutar wasannin Olympics a birnin Erdos, kuma tsawon hanyar da za a bi zai kai kimanin kilomita 6.3.
Bayan da aka kawo karshen mika wutar wasannin Olympics a birnin Erdos, yau da yamma, za a mika wutar wasannin Olympics a birnin Baotou na jihar Mongoliya ta gida.(Lubabatu)
|